Dalilai da ke sa mace ta sami budadden gaba (Farji) | Mujallar isyaku.com

Sirrin rike miji Yanayin halittar farji tamkar robar danƙo ce wacce zata iya buɗewa idan aka yi mata talala, haka kuma  zata iya komaw...

Sirrin rike miji

Yanayin halittar farji tamkar robar danƙo ce wacce zata iya buɗewa idan aka yi mata talala, haka kuma  zata iya komawa ta haɗe, wato ta  tsuke bayan buɗewa. Tsokokin bangon  farji masu motsi ne kuma zasu  iya tsukewa ko buɗewa idan mace tayi yunkurin tayi hakan, wato idan ta motsa su ko matse su ta ciki. Buɗaɗɗen farji (loose vagina) ko buɗewar farji (vaginal looseness) wani yanayi ne dake shafar mata da yawa musamman lokacin juna biyu da kuma bayan haihuwa inda farji ke canza yanayin halittarsa  ya ƙara girma, wato ya zama buɗaɗɗen wuri kasancewar naman dake zagaye da farji mai yiwa zakari zobe lokacin jima'i ya saki  , tsokokin sun saki basu iya damƙar zakari yanda ya kamata lokacin saduwa. 

Kamar dai yanayin halittar fatar jikin mutum, wasu mutanen fatarsu nada tauri  kamar roba marar sauƙin budewa idan aka jata,  wasu kuma fatarsu nada laushi da sauƙin yin talala idan aka jata, kusan haka itama halittar  gaban mace take. Wurin haihuwa jinjiri na fitowa ne ta farji inda wurin ke buɗewa sosai domin jinjiri ya fito. Bayan wani lokaci da haihuwa  farji na komawa ya tsuke . Duk da haka , farji ba zai taɓa komawa ba kamar yanda yake ada ko kamar na macen da bata taɓa haihuwa ba (ko budurwa) , koda kau anbi hanyoyin magani , farji zai zamanto ya ƙara  girma kaɗan ko da yawa.
Yawan haihuwar mace, budewar gaba saboda tiyatar likita/ƙarin kofa a lokacin haihuwa (tear) da yawan yin jima'i yau da gobe, na daga cikin dalilan dake haddasa budewar gaban mace. 

Idan buɗewar farji tayi yawa  yana zama kalubabale ga ma'aurata. Zaya iya zama matsala a rayuwarsu ta jima'i . Saboda wannan yanayi na sanya raguwar ɗanɗanon jima'i ga mace da mijinta koma ya hana macen jin ƙoluluwar daɗi  (orgasm) lokacin saduwa. Dalilin faruwar haka shine ,  farji baya matse/riƙe zakari da  kyau, ta yanda za'a samu ɗanɗanon gugar fata-da-fata tsakanin ma'aurata biyu wanda jin  wannan guga shine  zai kai ma'auratan biyu  ga gamsuwa mai ƙarfi a lokacin jima'i.

Bugu da ƙari, wannan matsala  na iya saka mace cikin damuwa da jin cewa bata amsa sunanta na cikakkiyar mace ba saboda bata jin dadin saduwa kuma bata iya gamsar da mijinta da kyau. Hakan kuma zai iya sanya maigidan ya ƙara wani aure domin biyan buƙatarsa. Hakika gamsuwar aure itace saduwa mai daɗi tsakanin ma'aurata da zata samar da soyayya da zaman lafiya mai  ɗaurewa. Matsatstsen gaba (tight vagina) bakin gwargwado, yanayi ne mai kyau da zai iya ƙarawa mace gishirin  soyayya mai ƙarfi tsakaninta da mijinta.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
IDAN KA GAN WANI ABU NA FARUWA, HANZARTAB KA SANAR DA MU A ISYAKULABARI@GMAIL.COM
Name

'YANSANDA,1,AL-AJABI,22,AREWA,45,BIDIYO,147,BINCIKE,1,BIRNIN-KEBBI,375,BOLLYWOOD,2,BUHARI,10,DUNIYA,109,ENGLISH,27,FADAKARWA,126,FASAHA,14,FITACCEN LABARI,19,HOTO,175,HOTUNA,90,JAKAR MAGORI,1,LABARI,2979,NISHADI,282,OSCAR,2,Samaila Yombe,42,SANARWA,31,SHARHI,16,SIYASA,387,TARIHI,11,TSARO,353,WASANNI,18,
ltr
item
ISYAKU.COM: Dalilai da ke sa mace ta sami budadden gaba (Farji) | Mujallar isyaku.com
Dalilai da ke sa mace ta sami budadden gaba (Farji) | Mujallar isyaku.com
https://3.bp.blogspot.com/-BIACkadtvE0/W_mvESwWWsI/AAAAAAAATfQ/q1bdZPD0b34Lqxr7WlrqltOSAlnNZrNGwCLcBGAs/s400/waist.jpg
https://3.bp.blogspot.com/-BIACkadtvE0/W_mvESwWWsI/AAAAAAAATfQ/q1bdZPD0b34Lqxr7WlrqltOSAlnNZrNGwCLcBGAs/s72-c/waist.jpg
ISYAKU.COM
https://www.isyaku.com/2018/11/dalilai-da-ke-sa-mace-ta-sami-budadden.html
https://www.isyaku.com/
https://www.isyaku.com/
https://www.isyaku.com/2018/11/dalilai-da-ke-sa-mace-ta-sami-budadden.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy