Legit Hausa
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar
'yan kasuwar daga garuruwan Andare, Katenga, da Maiyama, na hanyar su ta zuwa
cin kasuwar shanu a jihar Legas lokacin da hatsarin ya ritsa da su. Rahoton NAN
ya bayyana cewar motar da ke dauke da 'yan kasuwar da shanunsu ta kwacewa
direba a kan hanyar Maiyama zuwa Koko, sannan ta wuntsila zuwa cikin daji.
Wani shaidar gani da ido, Garba Maiyama, ya shaidawa NAN
cewar, "mutane 15 daga cikin 'yan kasuwar dabbobin take su ka mutu kuma
tuni aka mika su ga iyalansu domin yi masu jana'iza kamar yadda Musulunci ya
tanada. "Babban abin tashin hankalin shine yadda a gida daya mutane 5 su
ka mutu a hatsarin.
"Bamu san abinda ya haddasa hatsarin ba gaskiya,"
a kalaman shaidar. Sai dai kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Kebbi, DSP
Danjuma Possy, ya shaidawa NAN cewar ya zuwa yanzu dai ba a sanar da su batun
hatsarin ba.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI