• Labaran yau


  Kotu ta ki bayar da belin Sheikh El-zakzaky, ta umurci DSS ta ci gaba da tsare shi

  An gurfanar da shugaban kungiyar Islamic Movement of Nigeria wanda ake fi sani da suna Shi'a Sheikh Ibrahim El-zakzaky tare da maidakinsa a gaban wata Kotu a garin Kaduna. Amma bayan zaman Kotun Mai shari'a Justice Gideon Kurada ya ki aminta da bukatar bayar da belin Zakzaky, wanda ya ce babu wadataccen shaidar rashin lafiya da wanda ake kara ya gabatar domin gamsar da Kotu a kan bayar da belinsa.

  Hakazalika Justice Gideon ya umarci hukumar DSS ta ci gaba da tsare Zakzaky har iya lokacin da za a yi wannan shari'a.

  An dage shariar har zuwa ranar 22 ga watan Janairu 2019. Zakzaky na fuskantar tuhumar tayar da hankalin jama'a, gudanar da taro ba bisa ka'ida ba, kisan kai da sauransu.

  DAGA ISYAKU.COM

  Copyright, do not copy and paste our news on your blog without expressed permission from us.

  Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com

  Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

  Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kotu ta ki bayar da belin Sheikh El-zakzaky, ta umurci DSS ta ci gaba da tsare shi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama