An kori safeton dansanda daga aiki domin wulakanta sakamakon kwankwadan barasa

Rundunar yansandan Najeriya ta yi ma wani safeton dansanda koran kare daga aikin dansanda sakamakon wulakanta, bayan hotunan bidiyo sun nuna shi a kafofin sada zumunta ya yi tatil da barasa. Bayan safeto janar na yansanda IGP Ibrahim K. Idris NPM mni ya gan wannan bidiyo, ya umurci kwamishinan yansanda na jihar Lagos domin ya gano tare da hukunta wannan batagarin safeto dan giya. Wannan safeto ya wulakanta ne a unguwar Akowonjo da ke Dopemu a jihar Lagos

Sakamakon haka ne kwamishinan yansanda na jihar Lagos CP Imohimi Edgal ya sa aka yi bincike da aka gano wannan dansanda da aka gane cewa safeto Kadima Useni ne mai lambar dansanda176219. wanda ke sashen yansandan kwantar da tarzoma na Mopol Base 22 da ke Ikeja.

An koreshi daga aiki ne bayan ya gurfana a gaban Kotun yansanda na cikin gida da ake kira Orderly Room, kuma Alkalin kotun ya same shi da laifi,sakamakon haka aka yi masa koran kare daga aikin dansanda a yau, ba pansho balle gratiti.

DAGA ISYAKU.COM

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without expressed permission from us.

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN