Korarren dansanda da ya jagoranci fashin Bankuna a garin Offa ya mutu a hannun yansanda

Korarren kofur na yansanda kuma madugun yan fashi da makami da suka kai harin fashi da ya yi sanadin mutuwar mutum 32 a garin Offa Michael Adikwu ya mutu.

Attoni janar kuma Kwamishinan shari'a na jihar Kwara  Mr. Kamaldeen Ajibade, SAN, ya shaida haka a zaman babban Kotun jihar Kwara ranar Laraba.

Ya ce yansanda sun gabatar da mutum biyar cikin mutane shida da ake zargi a takardar shigar da kara, ya kara da cewa shugaban yansanda sashen da ya gudanar da binciken lamarin Mr. Abba Kyari ne ya shaida wa Kotu haka.

Sakamakon haka ya zama wajibi a yi gyara a takardar shigar da kara, domin ba yadda za a yi karar matacce a cewar Atoni janar. Mr Abba Kyari dai bai kara haske a kan yadda aka yi madugun yan fashin ya mutu ba.

Wadanda aka gabatar a gaban Kotu sun hada da Ayoade Akinnibosun, Ibikunle Ogunleye, Adeola Abraham, Salaudeen Azeez da Niyi Ogundiran.

Michael Adikwu wanda korarren dansanda ne mai mukamin kofur a rundunar yansanda na jihar Kwara, ya jagoranci wani mumunan fashi da makami da aka kai kan wasu Bankuna a garin Offa da ke jihar Kwara yan watanni da suka gabata. Daya daga cikin harin fashi da makami mafi muni a tarihin Najeriya kuma wanda korarren dansanda ya jagoranta ranar 5 ga watan Aprilu 2018.

Rahotanni sun ce Michael Adikwu da kanshi ya jagoranci sauran yan fashin suka fara yada zango a caji Ofis na garin Offa, kuma ya harbe yansanda da ke sintiri a bakin caji ofis, daga bisani ya shiga ofis zuwa ofis a cikin caji ofis na yansanda a garin Offa yana harbe yansanda da ke bakin aiki a wannan ranar inda ya kashe akalla yansanda 12 shi kadai.

Daga bisani ne ya jagoranci sauran yan fashin zuwa Bankuna, kuma suka ci karensu ba babbaka ta hanyar harbe jama'a da basu ji basu gani ba har wajen mutum 20.

DAGA ISYAKU.COM

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without express written permission from us

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN