INEC ta fitar da ranar da za a yi zaben Gwamnoni da na yan Majalisa


Legit Hausa

Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), ya bayyana cewa zaben yanki a babbar birnin tarayya zai gudana ne a ranar 2 ga watan Maris, 2019, tare da na gwamnoni, da majalisar dokokin jiha. Ya kuma bayyana cewa za’a wallafa jerin sunayen yan takara na zabe a ofishinta na babbar birnin tarayya da kuma yankuna shida a ranar Laraba, 21 ga watan Nuwamba, 2018 (yau).

Yakubu ya bayyana hakan a lokacin ganawa da kwamishinonin zabe a dakin taro na hukumar da ke hedkwatar INEC, Abuja a yau Laraba. Yanzu Yanzu: Za’a yi zaben gwamna, da na majalisar jiha a ranar 2 ga watan Maris - INEC Ya roki jama’a da su duba cikakken bayanai na yan takarar da suke neman wakiltansu.

An kammala zaben fidda gwani na yankunan a ranar 27 ga watan Oktoba 2018, INEC ta bayyana. Bayanan na kunshe ne a wasu rubutu da hukumar INEC din ta wallafa a shafinta na twitter @inecnigeria.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN