Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana jimaminsa kan kisar da
mayakan Boko Haram suka yiwa sojojin Najeriya a kauyen Metele da ke jihar Borno
inda ya tabbatar da cewa za a dauki matakan kare afkuwar hakan a gaba. Kalaman
na shugaban kasar yana zuwa ne kwanaki shida bayan mummunan harin ta bakin mai
magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu. Mr Shehu ya ce, "Shugaba
Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da mayar da hankali wajen tsare
lafiyar jami'an soji da ma sauran al'ummar kasar baki daya.
A cewar shugaban kasar, "Babu wani shugaba da zai nade
hannu yana kallo 'yan ta'adda suna barazana ga rayyukan jami'an soji da sauran
al'umma. Jami'an sojin mu sun nuna bajinta da jarumta a kan yan ta'adan kuma
zamu cigaba da basu dukkan gudunmawar da suke bukata domin kawo karshen wannan
masifar. A cikin kwanakin nan, zan cigaba da aiki tare da shugabanin soji da
shugabanin hukumomin tara bayyanan sirri domin sannin matakin da za a
dauka."
"Shugaban kasar
ya bayyana cewa yaki da rashawa matsala ce da ta zama ruwan dare a kasashen
duniya wadda ke bukatan hadin gwiwa tsakanin kasashen da ke fama da fitinar.
"Shugaba Buhari ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa gwamnatinsa ba zata
karaya ba wajen cigaba da yaki da rashawa da dorawa kan nasororin da aka samu a
kan yan ta'addan.
"Ya kuma
shawarci yan Najeriya su guji jefa siyasa cikin al'amarin inda ya ce dakarun
sojin Najeriya sun sadaukar da rayuwarsu ne domin samar da tsaro ga dukkan 'yan
Najeriya." A baya, Legit.ng ta kawo muku cewa a kalla sojoji 118 ne suka
rasa rayukkansu sakamakonn harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a
ranar 18 ga watan Nuwamba a sansanin soji da ke Metele a jihar Borno.
An kuma tabbatar cewa
har yanzu akwai wasu sojoji 153 da ba a gano inda suke ba kimanin mako guda
bayan harin da aka kai a sansanin na sojin kamar yadda wasu manyan shugabanin
soji suka fadi
Legit Hausa
Legit Hausa
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI