• Labaran yau


  Yan sanda sun kama miyagun yan fashi da makami 4 a Jigawa sun kwato bindigogi

  Rundunar yan sandan jihar Jigawa a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba sun ce sun kama wasu manyan yan fashi hudu a karamar hukumar Gwaram dake jihar.

  Kwamishinan ýan sandan jihar, Mista Bala Senchi, ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Dutse, sannan ya bayyana cewa ýan ta’addan sun addabi mazauna yankin. Senchi ya bayyana cewa jami’an rundunar yan sandan Federal Special Anti-Robbery Squad (FSARS) ne suka kama su a ranar 26 ga watan Satumba bayan sun samu tsegumi daga majiya abun dogaro.

  Ya bayyana cewa za’a hukunta hudu daga cikin tawagar da suka tsere, inda ya bayyana cewa laifinsu ya saba ma sashi na 96 da 296 na doka. Senchi ya kara da cewa tawagar sun sha kai hare-hare da dama a kauyukan Ranbazau,

  Yadda da kuma Sara dake yankin inda suka sace dukiyoyi da kudade. Daga cikin kayayyakin da aka kwato harda bindigogi na gargajiya da ak47 guda biyu. 


  Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

  Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

  hausa.naija.ng
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yan sanda sun kama miyagun yan fashi da makami 4 a Jigawa sun kwato bindigogi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama