An kama ja'iri yana lalata da mata kanana a tare saboda ya ba kowace N50

Yansanda sun damke wani Dan kasar Togo da laifin lalata da kananan yammata. Naira hamsin hamsin yake basu a duk lokacin da zaiyi lalata dasu. Hukumar yan sandan Ejigbo ne suka kama Dominic Samson mai shekaru 31 a duniya a ranar litinin bayan da mahaifin daya daga cikin yammatan mai shekaru 15 ya kawo kara.

Mai magana da yawun hukumar yan sandan, CSP Chike Oti, yace makwafta ne suka kama Samson na lalata da yarinyar mai shekaru 15 a lamba 28 titin Olusesan, Ejigbo. Makwaftan sun sanar da mahaifin yarinya wanda ya tafi wurin aiki.

Daga baya ne yazo ya sanar da hukumar yan sandan. Oti yace : Bayan kawo karar, DPO wacce mace ce tayi wa yarinyar tambayoyi kuma ta tabbatar da rahoton.

 "Ta tabbatar da cewa ba wai lalata kadai yake da yarinyar ba, har ta dubura yake saduwa da ita." "Yarinyar ta bayyana ba da ita kadai yake lalata ba. Har da wasu yara biyar masu shekaru tsakani 13 zuwa 15."

 "An kawo sauran yaran inda akayi musu tambayoyi kuma suka tabbatar da hakan. Yammatan sunce wanda ake zargin na basu Naira hamsin hamsin ne bayan ya gama lalata dasu."

Kamar yanda yace, an kai yaran asibiti inda rahoton likita ya nuna duk an lalata su. Kwamishinan yan sandan, Imohimi Edgal, ya shawarci iyaye da su dinga kula da yaransu domin wannan ne kadai mafita.


Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

hausa.naija.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN