Type Here to Get Search Results !

Yadda aka kashe wani saurayi a tawagar motocin Gwamnan jihar Sokoto

Hoton saurayi da aka kashe a wani tashin hankali da ya rutsa da tawagar Gwamnan jihar Sokoto ranar Asabar ya bayyana. Saurayin mai suna Imran Ahmad Alkalanci ya rasa ransa ne yayin da ake zargin cewa harsashi ne ya same shi.

Bayanai sun ce Imran yana kan hanyarsa ta dawowa gida ne bayan ya ziyarci 'yanuwansa domin sada zumunci. Wani rahotu ya ce jam'iyyar PDP ta shirya wani gangami ne domin tarbon Gwamna Aminu Tambuwal wanda ya fadi a zaben fitar da gwani na neman takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP.

Gwamnan ya sami gagarumin tarbo daga jama'a bayan ya sauka a filin saukar jirage na Sultan Abubakar 3 da ke Sokoto. Amma yayin da suke cikin jerin gwanon motoci sai wasu 'yan daban siyasa dauke da muggan makamai suka afka wa ayarin motocin.

Hakazalika an banka ma wata mota da ke dauke da rubutun APC wuta a garin Bodinga kusa da Jami'ar jihar Sokoto.

Ala tilasa tawagar motocin suka yi burki sakamakon turjiya daga 'yan daba a Unguwar Gawon Nama da ke Sokoto kusa da gidan Aliyu Magatakarda Wamakko, sakamakon haka ya zama dole jami'an tsaro suka shiga tsakani kafin aka bude hanya domin tawagar Gwamna Aminu Tambuwal ta wuce zuwa gidan Gwamnati. 

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.
Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN