Bidiyon Gwamnan Kano yana karbar cin hancin Dala Miliyan $5

Yanzu nan mu ka samu labari cewa an saki bidiyon Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje yana karbar cin hancin kudi har Dala Miliyan 5 daga hannun wasu ‘Yan kwangila a cikin ofishin sa. Jaridar DAILY NIGERIAN ta fito da bidiyon Gwamna Abdullahi Ganduje cikin babbar rigar sa yana shake tsabar kudi na Dalar Amurka. Ana zargin cewa Gwamnan kan karbi Miliyoyin Dalolin kudi kafin ya bada kwangila a cikin Jihar Kano.

Jafar Jafar wanda shi ne ‘Dan jaridar da ya saki Bidiyoyin ya bayyana cewa akwai sama da Bidiyoyi 10 wanda ake ga Gwamnan yana karbar rashawa. Jafar yace akwai bidiyoyi 9 da su ka dauki fuskar Gwamnan yana wannan aiki. Tuni dai Gwamnan na Kano Abdullahi Ganduje ya musanya wannan zargi idan yace ‘Yan adawa ne ke yi masa makarkashiya ganin siyasa ta gabato. ‘Dan jaridar da ya saki wannan bidiyo yace sam babu siddabarun fasaha a lamarin.

An dai dauki wannan bidiyo ne tun a farkon bara lokacin da wani dan kwangilar yayi amfani da wata na’urar daukan hoto a boye ya dauki bidiyon Gwamnan tsama-tsamo, sai dai yanzu ne aka sake su Duniya yayin da ake shirin zabe.



Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

hausa.naij.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN