• Labaran yau


  Wai sai baba ta gani: Minista ya garzaya kotu maimakon ya sauka daga mukaminsa

  Ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya maka hukumar NYSC kotu sakamakon rashin Kiran shi da bata yi bata 1979 wanda hakan ne bai bashi damar hidimtawa kasar shi ba na shekara daya.

  Ministan ya bukaci kotun da ta yanke hukuncin cewa hukumar NYSC ta yafe mishi wajabtacciyar hidimar ta shekara daya saboda ita ce bata kira shi ba a 1979 bayan da ya kammala karatu a makarantar shari'a ta Najeriya.

  Ya kaisu gaban kuliya ne bayan da jam'iyyar APC ta hana shi tsayawa takarar shugabancin jihar Oyo bayan da ta gano ya tsallake wajabtacciyar hidimar kasa ta matasan da suka kammala jami'a masu shekaru kasa da 30.

  Shittu ya roki kotun da ta hana NYSC da sauran masana shari'a da Kiran shi domin hidimar kasa. Ya roki kotun da ta umarci hukumar NYSC da ta bashi takardar shaidar hidimar kasa.

  "Nayi wa kasa hidima a matsayin Dan majalisar jihar Oyo bayan na kammala makaranta shari'a ta Najeriya." inji Adebayo. Read more: https://hausa.naija.ng/1198600-abin-dariya-minista-ya-garzaya-kotu-maimakon-ya-sauka-daga-mukaminsa.html

  Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

  Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

  hausa.naija.ng
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wai sai baba ta gani: Minista ya garzaya kotu maimakon ya sauka daga mukaminsa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama