Yansanda sun kama wadanda suka saci wata gawa a Asibiti

Abun mamaki baya karewa a cikin Duniyar nan tamu, wasu labaran sai su baka sha'awa wasu kuma su baka haushi, wasu kuma sai su cika ka da mamaki. Mai karatu zai yi mamakin jin cewa jakar magori ta leka jihar Imo ne, inda ta samo labarin wasu mutum biyu,  Chukwudi Chukwu dan shekara 38 da Bethel Lazarus dan shekara 28 wadanda suka saci wata Gawa daga Mutuware na wani Abibiti mai suna Jesus Hospital a garin Umuduruegbo Ugirike na karamar hukumar Ikeduru ranar 04/09/2018.

Babu wanda ya san musabbabin da ya sa wadannan mutane suka aikata wannan aiki, amma asiri ya tonu ne bayan an kula cewa wata gawa ta bace daga cikin gawakin da ke aje a Mutuwaren wannan Asibiti. Sakamakon haka aka rada wa yansanda da suka shiga binciken da ya kai ga damke wadannan mutane guda biyu tare da motar da suka sace gawar da ita kirar Suzuki Bus mai lamba RLU – 91 – XA.

Tuni mutanen suka amsa laifinsu a wajen yansanda kuma suka kai yansanda wajen da suka ajiye gawar a wani gandu a Umunjam Mbieri na karamar hukumar Mbaitoli a jihar Imo.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN