A cikin satin da muka yi bankwana da shi ne tsohon
mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya koka kan cewar ana yiwa rayuwarsa
da ta iyalinsa barazana saboda burinsa na son yin takarar shugaban kasa a zaben
2019.
Sai dai jam’iyyar adawa ta PDP ta ce babu wanda zata yi
zargi idan ba jam’iyyar APC ba matukar wani abu ya samu daya daga cikin ‘yan
takarar ta. A jawabin da PDP ta fitar ta bakin Kola ologbondian, sakataren yada
labarai na jam’iyyar, ta ce ba zata taba daukan batun barazana kan rayuwar
Atiku da wasa ba tare da yin kira ga shugaba Buhari day a bayar da umarnin
gudanar da bincike a kan dukkan koarfe-korafen da Atiku ya aike masa a rubuce.
Ologbondian ya
bayyana cewar tuni jam’iyyar APC ta shiga halin dimuwa da damuwa saboda irin
nagartar ‘yan takarar shugaban kasa da PDP ke da su tare da zargin gwamnati da
yin amfani da ‘yan banga da jami’an tsaro domin kuntatawa ‘yan takarar ta.
“Tun da jam’iyyar APC ta fahimci cewar dukkan ‘yan takarar
mu sun fi karfin Buhari suka fara amfani da karnukan farauta a cikin hukumomin
tsaro na gwamnati musamman ‘yan sanda, jami’an DSS da na hukumar EFCC domin
firgita ‘yan takarar mu dake son yin takara a zaben 2019. “Yanzu lamarin ya
wuce amfani da karfin gwamnati har ya kai ga yin barazana a kan rayuwar ‘yan
takarar mu. Muna son sanar da APC cewar babu abinda zai firgita mu ko ya saka
tsoro a zukatanmu,” a cewar Ologbondian.
Hausa.naij.ng
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI