Mun samu cewa cikin jiga-jigan 'yan siyasa dake fafutika
akan tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari, a yayin babban zabe da za a
gudanar a watan Fabrairun 2019, akwai wasu 8 daga cikin su da ake zargi da
laifin rashawa ta kimanin N232bn kamar yadda shafin jaridar The Punch na ranar
Asabar ta yau ya bayyana.
Binciken da manema labarai na jaridar suka gudanar ya
bayyana cewa, akwai dambarwar wannan zargi tsakanin jiga-jigan 'yan siyasar da
kuma hukumomin tsaro musamman hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta
EFCC. Hukumomin tsaron na zargin wannan jiga-jigan 'yan siyasa da aikata
laifukan rashawa ta almundahanar dukiyar gwamnati kama daga Naira miliyan dari
biyu har zuwa abinda ya kai Naira biliyan dari kan kowanen su.
Wasu daga 'yan siyasar takwas sun kasance mambobi na
jam'iyyun adawa musamman ta PDP, inda sauyin shekar su zuwa jam'iyyar APC ya
zamto wata tsarkaka tare da katanga tsakanin su da hukumomin tsaro masu gudanar
da bincike a kansu.
Jiga-jigan 'yan
siyasar takwas sun hadar da; Sanata mai wakilcin jihar Nasarawa ta Yamma,
Abdullahi Adamu, Sanata mai wakilcin jihar Sakkwato ta Arewa kuma tsohon
gwamnan jihar; Aliyu Magatakarda Wamakko da kuma tsohon shugaba marar rinjaye a
majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom; Sanata Godswill Akpabio
wanda a kwana-kwanan nan ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.
Sauran wadanda ake zargi da kashi a gindinsu sun hadar da;
tsohon gwamnan jihar Abia; Orji Uzor Kalu, tsohon sakataren gwamnatin tarayya;
Babachir Lawal, gwamnan jihar Zamfara; Abdulaziz Abubakar Yari, tsohon shugaban
jam'iyyar PDP na kasa; Ali Modu Sheriff da kuma tsohon gwamnan jihar Ribas kuma
Ministan Sufuri; Rotimi Amaechi wanda shine shugaban kungiyar yakin neman zaben
shugaba Buhari.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng