Rahotanni da muke samu a yanzu na nuni da cewa akwai wasu
daga cikin masu neman takarar shugabancin kasar a zaben 2019, karkashin
jam'iyyar PDP, da ka iya janye wannan kudiri nasu kafin ranar zaben fitar da
gwani na jam'iyyar da zai gudana a wannan watan.
Wata majiya daga PDP ta shaidawa kamfanin jarida na Punch
cewa shuwagabannin jam'iyyar na kasa sun yi wani zama da masu neman tsayawa
takarar shugabancinnkasar a jam'iyyar, inda suka shaida masu cewa akwai bukatar
wasu daga cikinsu su janye, don bada dama ga zakakuran cikinsu.
A cewa majiyar, an kuma umarci yan takarar shugabancin
kasar, da su sanya hannu a takardar amincewa da duk wani sakamako da jam'iyyar
ta fitar na zaben fitar da gwani, don gujewa rabuwar kawuna bayan kammala
zaben. "Shuwagabannin jam'iyyar na kasa sun zauna da masu neman takarar
shugaban kasa a karkashin jam'iyyar, inda aka sanar da su cewa wasunsu dole su
janye daga takarar don bada dama ga zakakurai a cikinsu, da zasu iya jan daga
da shugaba Buhari a 2019.
"Don haka, ana
sa ran da yawa daga cikinsu zasu janye daga tsayawa takarar a wannan watan.
Haka zalika an umurce su da sanya hannu akan takardar yarjejeniya, kan amincewa
da sakamakon zaben fitar da gwani." Akalla mutane 10 ne suka sayi takardar
tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, da suka hada da: Atiku
Abubakar, Sule Lamido, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, Ahmed Makarfi, Ibrahim Hassan
Dankwambo da kuma, Attahiru Bafarawa. Sauran sun hada da: Kabiru Tanimu Turaki,
Datti Baba-Ahmed, Senator Bukola Saraki, Aminu Waziri Tambuwal da dai sauransu.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng