Wasu chiyamomin jam'iyar APC na kananan hukumomi 3 a jihar Zamfara sun rasu sakamakon hadarin mota tsakanin Makkah zuwa Madina a kasar Saudiya.
Wadanda suka rasu su ne Alh. Jafarau Gidan Sambo daga karamar hukumar Kaura Namoda , Alh. Mudi Mallamawa, karamar hukumar Shinkafi, da Alh. Abdullahi Shugaba Ruwan Dorowa daga karamar hukumar Maru.
Dukkansu suna kan hanyarsu ce ta zuwa Madina daga Makka tare da sauran fasinjoji yayin da motar Bas da suke ciki ta sami hadari da karfe 3 na ranar Juma'a.
Uku daga cikin sauran fasinjan motar sun tsira, yayin da wadanda aka ambato a sama suka riga mu gidan gaskiya.
Mahukunta a kasar ta Saudiya na iya abin da ya dace bisa tsarin doka, kafin a bizine mamatan.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira