NAIJ.com ta ci karo da wani labari, na wani mutumi da aka
cafke a wata majami'a dake garin Fatakwal, inda yake kokarin satar kudi a
akwatin da aka tanadar don jama'a su rinka jefa tallafinsu.
Wannan labarin dai ya yadu a kafafen sada zumunta na yanar
gizo, wanda wani ma'abocin kafar Facebook mai suna Ezekiel West Tamunominabo ya
rubuta a shafinsa.
Ma'abocin kafar ta Facebook, ya bayyana cewa an cafke
mutumin ne a lokacin da yake kokarin bude kwadon akwatin da wasu wayoyin karfe.
A cewar Ezekiel, har zuwa lokacin da aka cafke mutumin, ya samu nasarar ciro
Naira dari biyar ne daga akwatin.
Ya ce limamin majami'ar yayiwa barawon addu'o'i shiriya
bayan da mambobin majam'iar suka kama shi. Haka zalika, daga labarin na
Facebook, rahotanni sun bayyana cewa mutumin ya dade yana aikata irin wannan
laifi.
An taba samunsa da aikata makamancin laifin a wasu majami'u
da dama "An cafke wani mutumi yana sata a a majami'ar Anjelika ta St.
Marks dake Fatakwal. A safiyar yau ne a a majami'ar Anjelika ta St. Marks, aka
cafke wani mutumi yana satar kudi a akwatin da mambobin majami'ar ke bada
tallafi.
Wanda zuwa lokacin da aka kamashi, ya samu nasarar satar
Naira 500 ne daga akwatin, daga rahotannin da aka tattara, mutumin ya dade yana
aikata wannan aika aikar, inda yake amfani da wayoyin karfe masu tsayi da kuma
sanya danko a karshensu don kamo kudin.
Limamin majami'ar ya yi ma mutumin addu'o'i, wanda ya yi
ikirarin cewa ya dade yana yin sata a majami'ar... Dama dai ance rana daya ta
barawo ce, rana daya kuma ta mai kaya. Rahoto daga Ezekiel Tomunominabo,
yammacin Fatakwa"
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng