Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa,
binciken kwararrun masana na kiwon lafiya ya bankado wata sabuwar hanyar amfani
da dafi na kudan zuma wajen warkar da miyagun ƙwayoyin cututtuka masu karya
garkuwar jiki.
Wani kwararren masanin kiwon lafiya na jami'ar Dar es Salam
dake can kasar Tanzania, Dakta Mkabwa Manoko, shine ya bayyana hakan yayin
ganawarsa da manema labarai bayan halartar wani babban taro kan harkokin kiwon
lafiya da aka gudanar cikin babban birnin kasar nan na tarayya.
Duk da cewa ba boyeyyen abu bane ana amfani da ruwan Zuma
wajen warkar da rauni, wani sabon bincike ya kuma bayyana yadda za a iya amfani
da dafin kudan zuma wajen yakar kwayoyi na wasu miyagun cututtuka masu kassara
garkuwar jiki ta lafiyar Bil Adama. Dakta Manoko ya bayyana cewa, kudan zuma
yana fidda wani dafi da akan iya amfani da shi sakamakon karfin ikonsa wajen
yakar wasu kwayoyin cututtuka masu karya garkuwar jiki irin su cutar kanjamau.
A sanadiyar haka kwararren likitan ya yi kira ga gwamnatocin
Afirka akan su mike tsaye wajen wajen horas da al'ummominsu da kuma masana
kimiya akan harkokin kiwon kudan Zuma domin tatsar wannan tabarraki da ya
kunsa. Manoko ya kara da cewa, akwai kimanin mutane miliyan biyu masu kiwon
kudan zuma baya ga cibiyoyi da dama na gudanar da bincike akan kudan zuma gami
da jami'o'i masu horaswa kan kiwon wannan kwari masu fa'idar gaske.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naija.ng
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI