Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadama rundunar yan sandan
Najeriya, hukumar zabe mai zaman kanta da sauran hukumomin tsaro a kasar da su
bari yan Najeriya su yi zabin ransu a zaben 2019 ba tare da kowani irin
barazana ba.
Shugaban kasar ya bayyana cewa shi ma ya amfana daga zaben
gaskiya da amana, bayan ya sha kaye sau uku, baya tsoron yin zabe na gaskiya da
amana a shekara mai zuwa. Ya sake ba da tabbacin jajircewarsa domin tabbatar da
cewa zaben 2019 a karkashin gwamnatinsa ta zamo na gaskiya da amana.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Buhari ya nuna rashin
jin dadinsa kan yadda kafofin watsa labarai ke rikon lamarin rikicin makiyaya
da manoma a kasar sannan ya bayar da shawarar cewa kafofin watsa labarai suyi
kokari su nemi sanin tarihin abun Da yake Magana a wani taron tattaunawa day an
Najeriya a Beijing, China a jiya Buhari yayi alkawarin cewa yan Najeriya da
suka kai matsayin zabe za’a bari su zabi san ransu.
A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Buhari ya amince da wasu
sabbin nade-nade guda hudu da suke da alaka da kamfanin nan na gwamnatin
tarayya dake bugawa tare da tsare takardun sirri watau Nigerian Security
Printing and Minting Company. Kamar yadda muka samu, Shugaba Buhari din ya nada
Alhaji Abbas Umar Masanawa a matsayin babban manajan Daraktan kamfanin tare
kuma da wasu manyan daraktocin sa su biyu.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng