Type Here to Get Search Results !

Jihohin Najeriya da PDP za ta gamu da cikas game da 2019


Mun samu labari cewa rikicin siyasa na nema ta rutsa da babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a wasu Jihohin Arewa. Wadannan Jihohi sun hada da Kano da kuma Kogi, Sokoto da Jihar Benuwai.

1. Kano A Jihar Kano kun ji labari cewa an fara samun takaddama tsakanin ‘Yan Kwankwasiyya da kuma manyan PDP a Jihar irin su Malam Ibrahim Shekarau, Aminu Wali, Bello Hayatu Gwarzo da sauran su. Shekarau da Kwankwaso su na neman Shugaban kasa

2. Sokoto Da alamu dai PDP za ta shiga rikici a Jihar Sokoto bayan Gwamnan Jihar Aminu Tambuwal ya sauya sheka. Tambuwal zai samu matsala wajen takarar Shugaban kasa, sannan kuma akwai rikici tsakanin sa da tsohon Gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa.

3. Benuwai A Jihar Benuwai ma dai za a buga rikici a 2019. Gwamna Ortom ya sauya sheka daga APC kwanaki inda yake neman zarcewa a PDP. Hakan ya kawo rabuwar kai a PDP wanda ya ja har wasu ‘Yan takara su ka fara komawa Jam’iyyar APC a Jihar.

4. Kogi A Jihar Kogi ana samun rabuwar kai tsakanin ‘Ya ‘Yan Jam’iyyar PDP. Sanata Dino Melaye na APC ya koma PDP inda zai nemi Jam’iyyar ta basa tikitin sake tsayawa kujerar Sanata a Jihar. Sai dai hakan na neman kawo rikici a Jam’iyyar adawar a Kogi.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naij.ng

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN