Baya ga yan takarar kujerar shugaban kasa, jam’iyyar bata
ambaci wani kwamiti da zai yi duba ga takardun sauran yan jam’iyya. Tuni dai
yan takara da dama sun yanki fam din takarar shugabancin kasa a karkashin
jam’iyyar inda suke jira a kaddamar da kwamitin.
Daga cikin yan takaran da suka yanki fam dinsu sun hada da
tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar Kano,
Sanata Rabiu Kwankwaso, Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, da kuma gwamnan
jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo. Har ila yau akwai tsohon gwamnan jihar Jigawa,
Alhaji Sule Lamido, tsohon ministan ayyuka na musamman, Alhaji Tanimu Turaki;
tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau; Attahiru Bafarawa da kuma Dr Ahmed
Datti.
Babban sakataren labaran jam’iyyar, Mista Kola Ologbondiyan,
ya fadama majiyarmu cewa a ranar Lahadi cewa babu laifi a cikin jinkirtawan,
cewa jam’iyyar zata gabatar da mambobin kwamitin ba da dadewa ba. Ya bayyana
cewa jam’iyyar ta mayar da hankali wajen siyar da fam dinta, cewa da zaran an
kammala da wannan kwamitin masu ruwa da tsaki zata saki sunaye.
A wani lamari na daban, mun ji cewa alkalin alkalai kuma
ministan shari’a, Mista Abubakar Malami ya kalubalanci hukuncin babban kotun
tarayya na sauraron karar dake bukatar a dakatar da tsige Dr Bukola Saraki a
matsayin shugaban majalisar dattawa. Ministan shari’an ya bukaci babban kotun
da tayi watsi da karar da tsoffin sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress
(APC), Rafiu Adebayo da Isa Misau suka shigar a gabanta.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng