Majalisa ta fara gyaran dokar zabe da Buhari ya yi watsi da ita sau 2


Majalisar tarayya ta fara aikin kan kudirin yin garambawul ga dokar zabe na 2010 da shugaba Muhammadu Buhari ya ki saka hannu a kai saboda wasu matsaloli da ya ke son majalisar ta gyra.

Mambobin majalisar dattawa da na wakilai na kwamitin gyarar dokar zaben ne suka bayar da sanarwan a yau Litinin a Abuja inda suka ce kwamitin ta fara zama domin duba dalilan da yasa shugaba Buhari ya ki amincewa da kudirin domin su gyara.

A lokacin da ya ke magana da manema labarai kafin kwamitin ta shiga taron ta, Ciyaman din kwamitin INEC a majalisa, Sanata Suleiman Nazifi ya ce kwamitin na da babban nauyi a kanta saboda dukkan 'yan Najeriya sun sanya musu ido.

Nazif ya kuma ce wannan shine karo na hudu kwamitin za tayi aiki kan kudirin dokan wanda shugaba Buhari ya mayarwa majalisar har sau biyu. "Nayi imanin cewa aikin da mu keyi zai amfani 'yan Najeriya, Inji Nazif. Shugaba Buhari ya aike wasika ga shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara domin sanar da matsayarsa na kin amincewa da dokar.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naija.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN