Yan sanda sun yi magana game da dan siyasar da aka kama yana wanka da jini

Dazu ne dai muka kawo maku labarin wani dan majalisar jiha da wasu matasa a jihar Osun dake a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya suka cafke su dake zaman shugaban masu rinjaye a majalisar jiha Honorabul Timothy Owoeye yana wanka a tsirara cikin jeji. Source: Twitter Shi dai shugaban masu rinjaye a majalisar jiha Honorabul Timothy Owoeye, an ce wankan da aka kama shi yana yi baya rasa nasaba da tsafi irin na 'yan tsubbu da kan sa 'yan siyasa yi musamman ma ganin zabukan 2019 na kara karatowa. Kawo yanzu dai mun samu karin bayani daga jami'an yan sandan jihar inda suka ce lamarin ya faru ne kimanin watanni shida da suka gabata sannan kuma tuni har sun fara cafke wasu daga cikin matasan da suka tozarta dan majalisar. Yan sandan sun cigaba da cewa gadar zare ce aka shiryawa dan majalisar tare da hadin bakin wasu masu magnin gargajiya wadanda suka umurci dan majalisar da ya je yayi wanka tsirara domin samun nasara a siyasar sa. Suka cigaba da cewa yan tsibbun haka zalika sai suka hada kai da wasu mutane inda suka zo suka dauki hotunan dan majalisar yana wanka sannan kuma suka bukaci ya rika basu kudi akai akai idan dai baya so su tona masa asiri. NAIJ.com dai ta samu cewa matasan sun dauki hoto da bidiyon dan majalisar yana tsakiyar wanka da jinin ne suka kama shi duk da dai kawo yanzu ba'a tabbatar da jinin mutane ne ba ko kuwa na dabba. Da dan majalisar dai yaga dubun tasa ta cika shine ya baiwa matasan makudan kudade domin su rufa masa asiri amma daga baya kuma suka fallasa maganar. Read more: https://hausa.naija.ng/1192604-yan-sanda-sun-yi-magana-game-da-dan-siyasar-da-aka-kama-yana-wanka-da-jini.html#1192604

Dazu ne dai muka kawo maku labarin wani dan majalisar jiha da wasu matasa a jihar Osun dake a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya suka cafke su dake zaman shugaban masu rinjaye a majalisar jiha Honorabul Timothy Owoeye yana wanka a tsirara cikin jeji.

Shi dai shugaban masu rinjaye a majalisar jiha Honorabul Timothy Owoeye, an ce wankan da aka kama shi yana yi baya rasa nasaba da tsafi irin na 'yan tsubbu da kan sa 'yan siyasa yi musamman ma ganin zabukan 2019 na kara karatowa. Kawo yanzu dai mun samu karin bayani daga jami'an yan sandan jihar inda suka ce lamarin ya faru ne kimanin watanni shida da suka gabata sannan kuma tuni har sun fara cafke wasu daga cikin matasan da suka tozarta dan majalisar.

Yan sandan sun cigaba da cewa gadar zare ce aka shiryawa dan majalisar tare da hadin bakin wasu masu magnin gargajiya wadanda suka umurci dan majalisar da ya je yayi wanka tsirara domin samun nasara a siyasar sa. Suka cigaba da cewa yan tsibbun haka zalika sai suka hada kai da wasu mutane inda suka zo suka dauki hotunan dan majalisar yana wanka sannan kuma suka bukaci ya rika basu kudi akai akai idan dai baya so su tona masa asiri.

NAIJ.com dai ta samu cewa matasan sun dauki hoto da bidiyon dan majalisar yana tsakiyar wanka da jinin ne suka kama shi duk da dai kawo yanzu ba'a tabbatar da jinin mutane ne ba ko kuwa na dabba. Da dan majalisar dai yaga dubun tasa ta cika shine ya baiwa matasan makudan kudade domin su rufa masa asiri amma daga baya kuma suka fallasa maganar.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naij.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN