Kebbi: Kansilolin karamar hukumar Yauri na yunkurin tsige shugaban karamar hukumar

Yanzu haka a garin Yauri na jihar Kebbi, hankalin jama'a ya karkata ga Sakatariyar karamar hukumar Yauri, sakamakon wani labari da ke nuna cewa Kansilolin karamar hukumar suna wani yunkuri na tsige shugaban karamar hukumar  Hon.Musa Muhammad (Stone) sakamakon wasu laifuka da suke tuhumarsa da aikatawa.

Amma a zantawarmu da Pamanent Sakatare na Ma'aikatar kananan hukumomi da harkokin Sarauta na jihar Kebbi, ya shaida mana cewa a daidai lokacin da muka tuntube shi da wannan zance yana Ofis har ma da Kwamishinan Ma'aikatar, amma fa su kam ba wata takarda ko labari da ya zo masu dangane da wannan zance na Kansilolin Yauri da shugaban karamar hukumarsu.

Wakilinmu daga karamar hukumar Yauri, Real Sani 2effect Yauri, ya samo takardu da aka ce sun fito daga hannun kansilolin dauke da zargi da suke yi akan shugaban karamar hukumar.

Ga Laifuka har guda bakwai da suke tuhumar sa kamar haka:
1.Rashin zama Karamar hukumarsa domin jin korafe korafe talakawansa
2.Kashe Naira milliyan ukku da dubu Dari biyar na (over head code) ba bisa ka idaba.
3.Gwamnati ta ware kudin aikin hanyar lokos har naira million hudu da dubu dari hudu amma bai gudanarda aikin ba.
4.Gwamnati ta ware kodi domin gyaran mototocin karamar hukumar Tiffer hilux bulldozer amma ya sayarda motocin batare da yin gyaranba.
5.gwamnati ta bada naira milliyan daya da dubu Aba mallamai addini amma yabasu dubu dari biyu.
6.Gwamnati ta bada kudi Aba malaman zabe wato Inec domin ayi ma mutane rejista amma bai ba suwaba.
7.Baida kyakkyawar Alaka da talakawansa ga karya dokar aiki.

Kansilolin da suka saka hannu domin tsige shugaban karamar hukumar nasu karkashin jagorancin shugaban kansilolin Shehu Umar (Tatta'u)Sune kamar haka:

1.Ahmad Adamu
2.Shehu umar
3.Alhassan Adamu
4.Abdullahi Adamu tondi
5.Murtala sale
6.Atiku isyaku
7.Abdul malik kasimu
8.Rashidu Kasimu
9.Rayyanu waziri
10.Husai Muhammad

Yunkuri da muka yi domin samun shugaban karamar hukumar Yauri domin jin ta bakinsa ya ci tura,haka zalika mun kasa samun jagoran Kansilolin da ke wannan yunkuri Shehu Umar (Tatta'u) a wayar salula kafin lokacin rubuta wannan rahotu.

Daga Isyaku Garba da Real Sani 2effect Yauri

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN