Karanta abun kunya da ya zubar da mutuncin mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe

Isyaku Garba | Rahotun musamman | 12-9-2018 |


Shugaba Muhammadu Buhari Dattijon arziki ne mai nagarta a idanun jama'ar Najeriya ciki har da makiyansa, sun tabbatar Dattijo ne wanda baya cin amana kuma baya hana jama'a hakkinsu. Sakamakon wadannan halaye ya tsaya a karkashin jam'iyar APC a zaben 2015 kuma ya lashe zabe ta hanyar kayar da shugaban kasa a wancan lokaci Goodluck Jonathan. Dubu dubatan mugayen mutane da maketata sun bi rigar alfarma ta shugaba Buhari a karkashin jam'iyar APC suka lashe zabe ba  wai domin nagartarsu ba, amma saboda nagartar shugaba Buhari.

Bayan tafiya ta yi tafiya, halayen mutane masu alamar ayan tambaya a mutuncinsu ya fara bayyana, kama daga cin amanar talaka, rashin biyan albashin ma'aikata da gangan, al'mubazzarantar da dukiyar jama'a, ko hana sauran jama'a shigowa gwamnati a dama da su duk da yake su ne suka sha bakar wahala domin ganin wadanda ke kan mulki sun yi nassara.

A jihar Kebbi, Mataimakin Gwamnan jihar Samaila Yombe Dabai ne ya kantama wani abun kunya da ya zubar da mutuncinsa, har da mutuncin Gwamnatin jihar Kebbi sakamakon wani bincike da muka yi dangane da wani lamari, ganin cewa shi ne mutum na biyu a bisa sikelin daraja na shugabancin jihar bayan Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu. Ala kulli hali, shi shugaba ya tabbatar wa talakansa cewa shi shugaba ne, haka zalika, bayan nuna kwarewar shugabanci, sai ya nuna  dattaku wajen tafiyar da hulda tsakaninsa da talakansa.

Duk da yake a bayyane yake karara cewa akwai yar tsami tsakanin Gwamnatin jihar Kebbi da duk wani abin da ya shafi yan jarida, manema labarai ko mawallafa sakamakon labarai da suka bayyana a shafukan labarai da dama inda yan jarida suka turje wa Gwamnati a yan watannin baya, wanda sakamakon haka wani hadimin Gwamnan jihar Kebbi kuma babban Sakataren watsa labarai na Gwamnatin jihar Kebbi ya fitar da sanarwa amadadin Gwamnatin jihar Kebbi yana zargin yan jarida da kin yin aikinsu, rashin nuna kwarewa wajen tafiyar da aiki har ma barazana ya yi cewa duk dan jarida da baya bukatar aiki da su ya sauka lafiya kafin daga bisani Gwamnati ta zauna da su yan Jarida a gidan Gwamnati kuma aka fahinci juna.

A watan Satumba na 2017, Mataimakin Gwamanan jihar Kebbi Saamaila Yombe Dabai ya bukaci ISYAKU.COM ya zo domin ya yi masa aiki bayan ya zargi sashen aikin jaridarsa da rashin kwarewa a bisa taffiyar da labari na zamani, musamman wanda ya shafi yanar gizo. Bisa kwarewar Kampanin Seniora International a kan wanannan sashe, ISYAKU.COM ya shiga yi wa Mataimakin Gwamna Samaila Yombe aiki tsakani da Allah bayan an ci ma wata yarjejeniya a cikin Ofishin Mataimakin Gwamna Samaila Yombe.

Sakamakon wannan yarjejeniya na fatar baki, bisa la'akari da matsayi da shekarun Mataimakin Gwamna Samaila Yombe ISYAKU.COM ya shiga aiki gadan-gadan kuma tsakani da Allah. A cikin wata shida, daga watan Satumba 2017 zuwa watan Aprilu 2018 Yombe ya biya ISYAKU.COM kudin wata biyu ne kacal. Bayan koke ta fatar baki kai tsaye zuwa ga Yombe domin a biya sauran kudaden domin a ci gaba da gudanar da aiki, amma Yombe bai mayar da martani ba. Bayan haka, aka sake aika sakonnin SMS har sau uku ana tunatar da shi a kan lamarin, wannan ma ya ci tura. Daga karshe sai aka aika masa sako na Whatsapp domin tunatarwa cikin ladabi, mutunci da biyayya, amma Yombe bai mayar da martani ba.

Sakamakon haka ISYAKU.COM ya kaurace wa aiki da Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe Dabai sakamakon rashin cika alkawari da biyan hakkin aiki da aka yi masa. Bayan yan kwanaki bai gan ISYAKU.COM ba a wajen aikinsa, sai ya bukaci sanin dalili kuma aka yi masa bayani cewa saboda ba'a biya kudin wajen wata hudu bane, ganin cewa ISYAKU.COM Mujalla ce mai zaman kanta tunda ba albashi gwamnati ma'aikatanta ke karba ba. Nan ma bai dau wani mataki ba domin ya biya hakkin da ya wajaba a kansa kasancewa kowa ya san cewa ISYAKU.COM yana yi masa aiki.

Ana cikin haka ne ISYAKU.COM ya fuskanci wata barazana sakamakon wani labari da muka wallafa, inda Samaila Yombe ya umarci mai taimaka masa watau PA dinsa mai suna Yakubu , cewa ya gaya wa ISYAKU.COM cewa ya kwashe kayansa ya bar jihar Kebbi kafin ya dawo Birnin kebbi daga Abuja bayan Kotu ta kori karar da Bello S. Yaki ya shigar a gabanta, wai domin ISYAKU.COM ya wallafa wani labari da bai yi ma Gwamnatin jihar Kebbi dadi ba, domin ya saka hoton gidan Gwamnatin jihar Kebbi a hoton da aka yi amfani da shi a labarin da sauran ababe.

Sakamakon haka ISYAKU.COM ya mayar da martani da ya zakulo bayanan cewa shi Yombe wasa ne yakeyi kuma bai umarci PA nashi Yakubu ya shaida wa ISYAKU.COM cewa ya kwashe kayansa ya bar jihar Kebbi ba. Wannan ne dalili da ya sa ISYAKU.COM ya saka muryar wannan PA domin tabbatar da abin da ya faru tsakani da Allah.

Tun kafin wannan lokaci, ISYAKU.COM ya tuntubi babban mai watsa labarai na jim'iyar APC na jihar Kebbi Alh. Sani Dododo, akan cewa ya yi wa Allah ya shiga tsakaninsa da Yombe domin ya biya shi hakkinsa, kuma Dododo ya tabbatar cewa ya tuntubi Yombe a kan lamarin, amma daga karshe dai ba wani bayani .Hakazalika ISYAKU.COM ya tuntubi wani jigo a jam'iyar APC na jihar Kebbi tare da wasu masu  ba Gwamna Atiku bagudu shawara domin su taimaka ya bayar da hakkin ISYAKU.COM amma lamarin ya faskara.

Daga karshe dai wani abin kunya ne ya faru, domin dai Samaila Yombe rubuto wata takarda ya yi kuma ya rattaba mata hannu ranar 2/7/1018 inda ya kalubalanci gabadaya aikin da ISYAKU.COM ya yi, ta hanyar wulakantar da martaba, mutunci da darajar lokaci da aka yi domin ganin am mutunta yarjejeniya da shi tun farko. Yombe ya yi kazafin cewa ISYAKU.COM ya wallafa labarai 29 ne kacal a tsawon wata kusan shida da ya yi tare da shi, har da rattaba hatiminsa watau ya sa hannu kuma tare da kwanan wata kamar yadda aka gani a kasa cikin wannan hoto.

Wannan lamari ya ba jama'a matukar mamaki ganin yadda gudan mataimakin Gwamnan jiha zai danne hakkin wanda ya yi masa  aiki tsakani da Allah kuma da zuciya daya domin ganin an yi nassara a manufar tafiya, amma aka saka masa da danniya har da barazana duk da cewa Yombe da ISYAKU.COM duk yan masarauta daya ne watau Masarautar Zuru.

Bisa dalilai da muka zana a sama, ISYAKU.COM yana tabbatar wa Duniya cewa, ba labari 29 ne muka wallafa wa Mataimakin Gwamna Samaila Yombe ba a cikin wata shida, mun wallafa labari fiye da 73 a ISYAKU.COM da Hausa kuma muka wallafa labarai fiye da 50 da Turanci a KEBBI24.COM bisa hujjoji da muka gabatar a kasa. Mun saka wasu labari da muka wallafa tun lokacin da muka fara yi wa Yombe aiki, kuma muna kalubalantar kowaye cewa ya saka daya daga cikin kanun labari da muka rubuta a Google ya bincika idan Google bai kaishi shafinmu na ISYAKU.COM wajen da labari yake ba. Hakazalika a labari na turanci.

Wata babbar matsala da wasu manyan jami'an Gwamnatin jihar Kebbi ke fuskanta shine na rashin iya banbancewa tsakanin Jaridu na kasa kamar su Dailytrust, Leadershi da kuma wasu shafuka da ba na kasa bane amma suna da matukar tasiri a jihohi da yankinsu da jama'ar su, domin a nan ne suke watsa labaransu kuma suna da dubban maziyarta shafin, kasancewa suna bayar da ingantaccen labari ba wai kawai kwashe zuba na Facebook ko Whatsapp ba. Wadannan shafuka ana kiransu News Blogs ko Online News Blogs, Online Publishers da sauransu wanda a halin yanzu Seniora International ce ke da cikakken rijista da Corporate Affairs Commission, kuma Ministry of Information & Culture ta san da zamanta a jihar Kebbi. Wanna Kampanin ke dauke da ISYAKU.COM,KEBBI24.COM da NEWSDAY24.COM.NG.

A kan wadannan hujjoji da muka gabatar, mun yi imani cewa Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe Dabai bai cika alkawari ba, kuma wannan ba girmansa bane, yayin da mai daraja na biyu a darajar shugabancin jiha ya zama wanda ya fadi abinda ba gaskiya ne ba ga talakansa har da sa hannu a takarda, wannan ya nuna yadda ake amfani da sunan shugaba Buhari domin a takura wa talaka, domin ba don darajar sunan shugaba Buhari ba , lallai da asirin wasu yan siyasa zai tonu a 2019.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN