'Yan bindiga sun kashe mutane 13 tare da raunata wasu da
dama a wata hari da suka kai a kauyen Badarawa da ke karamar Shinkafi ta jihar
Zamfara.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun far ma
kauyen ne da safiyar jiya yau Alhamis inda suka rika harbin dukkan wanda suka
hadu dashi kuma daga baya suka rika bi gidajen mutane daukan abinda suke so.
Duk da cewa Rundunar 'yan sanda na jihar Zamfara ta ce
mutane shida kawai aka kashe a harin, wata kwakwarar majiya daga kauyen ta ce
mutane 13 ne suka rasu sakamakon harin.Kakakin Rundunar 'yan sandan jihar,
Mohammad Shehu, ya tabbatar da afkuwar harin ga majiyar NAIJ.com amma ya ce
mutane shida aka kashe a harin.
"Rahotannin da muka samu sun nuna cewa mutane shida aka
kashe a harin, yayin da wasu 10 suka sami munanan raunuka. "Bayan an sanar
da mu abinda ke faruwa, mun garzaya kauyen cikin gagagwa tare da sojojin
Najeriya. Muna bin sahun 'yan bindigan a daji domin gano inda suke buya.
"Mun baza
jami'an sintiri a kauyen a yanzu kuma mutane sun fara cigaba da harkokinsu
kamar yadda suka saba," inji mataimakin sufritanda, Shehu. Tuni dai aka yi
jana'izar mutane da suka riga mu gidan gaskiya a harin na 'yan ta'adda.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI