Jam'iyyar APC ta karyata rahotan sashen kwararru kan tattalin
arzikin kasa (EIU) da HASBC, wani kamfani mai harkoki a kasashe kan bankuna da
kudade, rahoton da ke cewa zarcewar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019 zai
jawo mummunan karyewar tattalin arzikin Nigeria.
A cikin wata sanarwa da ta bayar a ranar Laraba, dauke da sa
hannun Yekini Nabena, Sakataren watsa labarai na jam'iyyar na kasa, APC ta ce
rahoton da kamfanin EIU ya fitar, na nuni da cewa jam'iyyar adawa ta PDP ce
zata lashe zaben 2019, da cewar gwamnatin gaba zata fuskanci babbar matsalar
tsaro. "Gwamnatin gaba zata fuskanci karyewar tattalin arzikin kasa (bayan
zaben 2019) wanda hakan ke nuni da cewa barazanar da tsaro ke fuskanta a kasar
zai zarce na yanzu" a cewar rahoton EIU.
Haka zalika rahoton ya bayyana cewa: "Muna kyautata
tsammanin samun karuwar matsalolin tsaro, ko da ya ke rundunar soji kwararru ne
a wannan bangaren" Jam'iyyar APC ta bukaci yan Nigeria da su kauracewa
wannan "hasashe da rahoton kamfanin" domin sanin su da kuma watsi da
su kasancewar ba su ne na farko da suka taba yin irin wannan hasashe ba, a
shekarun baya hukumomin kasashen turai sun sha fitar da irin wadannan
rahotanni.
A shekarun baya, an fitar da rahotannin cewa kasar Nigeria
zata wargaje a 2015, biyo bayan ballewar wasu kabilu da zasu bukaci samun
yancin cin gashin kansu. Sai dai, an doshi akalla shekaru 4 da wucewar shekarar
da akayi hasashen zata zamo shekarar rabuwar Nigeria, mai-makon ma kasar ta
rabu, sai ma kara dunkulewa da ta ke yi, yayin da gwamnatin shugaban kasa
Muhammadu Buhari ta maida hankali wajen samar da hadin kai a cikin kasar.
APC ta buga misali da gwamnatocin baya da suka gabata,
wadanda aka saci kudaden jama'a, gwamnatocin da suka mayar da wasu hukumomi
kamar karnukan farautarsu, irin su hukumar jarabawar share fagen shiga manyan
makarantu (JAMB), hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS) da kuma hukumar hana
fasa kwabri ta kasa (NCS). Jam'iyyar ta kuma bayyana takaicinta na yadda EIU ta
ki lura da irin kudaden da aka kwato daga barayin gwamnati, ta hanyar hukumar
EFCC.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI