'Yansanda sun kama group Admin na Whatsapp da wasu mutum 2

isyaku.com |11-9-2018 |

Hukumar yansanda a jihar Kano ta kama wasu mutum 3, na miji daya da matan aure 2 bayan an zarge su da watsa labarin karya a cikin group na WhatsApp da suke gudanarwa. Dukannin wadanda aka kama suna da aure.

Kakakin yansanda na jihar Kano Magaji Musa Maaji ne ya shaida wa manema labarai haka, yace "wata ma'aikaciyar gwamnati mai suna Mrs Bushirat Madaki ce ta gabatar da takardar koke ga hukumar, nan take kuma Kwamishinan yansanda ya umarci a gudanar da bincike da ya kai ga kamo wadanda ke shugabancin wannan group na WhatsApp,

Wadanda aka kama sun tabbatar da yada hoto da labarin da ake nuna cewa ita matar da aka saka hotonta a labarin wai tana fataucin yarane. Sakamakon haka matar ta gan lallai an bata mata suna ne kuma kuma haka zai sa jama'a su yi tunzuri da zai iya sa a kai mata farmaki da zai taba lafiya da mutuncinta".

Maaji ya bukaci masu amfani da kafofin sada zumunta cewa, su dinga yin taka tsan-tsan kuma su gudanar da bincike kafin su watsa kowane irin labari.

Wadanda aka kama dai tuni suka ba wanda aka yi ma kazafi hakuri, sun kuma tabbatar da cewa su fa basu taba ganin wannan mata ba, kawai an turo labarin ne a cikin wannan group kamar yadda yake a al'adar amfani da yawancin group na WhatsApp a fadin Najeriya.

Har yanzu dai yansanda na gudanar da bincike a kan lamarin, daga bisani dai an bayar da belinsu.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN