Shugaban kungiyar kwadago ta kasa, Ayuba Wabba, ya zargi
Gwamnatin tarayya da ministan kwadago, Sanata Chris Ngige da tsayar da karin
karancin albashin, yace ma'aikata bazasu cigaba da hakuri ba. Ansan cewa zuwa
21 ga watan Augusta na zasu kammala aikin da kwamitin karin karancin albashin,
amma sai Ministan Kwadago yace Gwamnatin tarayya bata shirya ba.
"Hakan na nuna cewa basu shirya tabbatar da karin
karancin albashin ba a ranar 4 da 5 ga watan satumba, duk da mu dai mun kammala
shirye shiryen mu " inji Wabba. " Za'a iya tunawa cewa, an nada
kwamitin ne tun a watan Nuwamba 2017 amma basu fara aiki ba sai a watan Maris,
akan dalilin da su kadai suka sani."
Kamar yanda tsarin aikin ya nuna, yakamata mu kammala ne
zuwa 21 ga watan Augusta, amma sai ya fada a ranar hutu Hakan yasa aka maida
zuwa 4 da 5 ga watan Satumba. A wannan taron ne yakamata mu kammala dukkan
rahoto, sannan mu kawo karshen aikin.
Amma kafin mu kammala
sai ministan kwadago, a matsayin wakilin Gwamnatin tarayya ya tashi yace suna
da bukata tataunawa kafin su tsayar da karancin albashin. Inji Wabba
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI