Dalilai 5 da suka sa APC ta kasa lashe zaben gwamnan Osun kamar yadda ta lashe na Ekiti


Magoya bayan APC, mai mulki, dake fatan jam’iyyar zata lashe zaben gwamnan jihar Osun cikin sauki kamar yadda tayi a jihar Ekiti, sun sha mamakin kashin da ta sha a hannun jam’iyyar PDP. Bayan kammala tattara sakamakon zaben na ranar Asabar, 22 ga watan Satumba, jam’iyyar PDP ta samu jimillar kuri’u 254,698 yayin da jam’iyyar APC ta samu jimillar kuri’u 254,345, banbancin kuri’u 353 kacal a tsakani.

Baturen zaben gwamnan na Osun, Joseph Afuwape, ya bayyana cewar tunda babu tazara mai yawa tsakanin dan takarar APC, Isiaka Oyetola, da na PDP, Ademola Adeleke, sai an sake zabe a wasu mazabu 7 dake kananan hukumomi 4.

Jaridar naij.com tayi nazari tare da zakulo dalilan da suka sa jam’iyyar APC ta kasa taka muhimmiyar rawa a zaben na ranar Asabar kamar yadda aka yi zato.

1. Rashin biyan albashin ma’aikata Babban dalilin da ya sa jama’ar jihar Osun bijirewa jam’iyyar APC a zaben gwamna shine matsalar rashin samun albashi. Matsalar albashi c eta kayar da PDP a zaben gwamnan jihar Ekiti. Tun a watan Yuni na shekarar 2015 gwamna Rauf Aregbesola ya bullo da tsarin biyan ma’aikatan jihar Osun rabin albashinsu bayan jihar ta shiga matsin tattalin arziki.

2. Rigingimun cikin jam’iyya Har zuwa ranar Asabar da aka gudanar da zaben gwamna a Osun, jam’iyyar APC ba ta yi sulhu tsakanin ‘ya’yanta da suka yi fushi ba bayan kammala zaben fitar da dan takara.

3. Dan takarar PDP PDP ta zabi Sanata Ademola Adeleke ne a matsayin takararta saboda irin farinjinin da gidansu keda shi a siyasar jihar Osun. Ademola Adeleke ya zama sanata ne bayan mutuwar dan uwansa Isiaka Adeleke. Hakan ta faru ne saboda irin kaunar da mutanen Osun ke yiwa ahalin gidan Adeleke

4. Siyasar Dalibai Daliban jami’ar kimiyya ta Ladoke Akintola (LAUTECH) na taka muhimmiyar rawa a siyasar jihar Osun da Oyo. LAUTECH jami’a c eta hadin gwuiwa tsakanin gwamnatin jihar Osun da Oyo. Yadda gwamna Rauf Aregbesola na jihar Osun ya gaza biyan bukatun daliban jami’ar, ya matukar fusata matasan tare da jawowa jam’iyyar APC bakinjini.

5. Yawan ‘yan takara masu jama’a Bayan ‘yan takarar APC da PDP, akwai ‘yan takara biyu masu farinjin a zaben na ranar Asabar. ‘Yan takarar su ne; tsohon mataimakin gwamna a jihar, Sanata Iyiola Omisore, da kuma Moshood adeoti, tsohon sakataren gwamnatin jihar da ya fice daga APC bayan ya fadi zaben cikin. Adeoti, dan takarar jam’iyyar ADP, ya samu kuri’u 49,726 a sakamakon zaben da hukumar INEC ta bayyana a jiya, Lahadi.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naija.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN