Ba wata yarjejeniyar sirri tsakanina da Yombe kan tsayawa ta takara - Kabiru Tukura

Isyaku Garba | 23-9-2018 |

Fitaccen matashi dan takarar kujerar dan Majalisar Wakilai na tarayya mai wakiltar Zuru, Fakai, Danko/Wasagu da Sakaba a Majalisar Wakilai na tarayya Alh Kabiru Tukura, ya musanta jita-jitar cewa an gudanar da tattaunawar sirri tsakaninsa da Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi dangane da aniyarsa na takarar mukamin dan Majalisar Wakilai.

Tukura ya sanar da haka ne yayin wata tattaunawa da wakilinmu ta wayar salula ranar Lahadi. Ya ce " Mai girma mataimakin gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe bai tuntube ni ba a sirrance dangane da zancen tsayawata takarar mukamin da nike nema. Amma tabbas na tuntube shi dangane da aniya ta na tsayawa takarar kujerar dan Majalisa, kuma na ji dadin yadda ya tarbe ni tare da shawarwari da ya bani a matsayinsa na uba.

Tabbas jama'ar kasar Zuru, Fakai, Danko/Wasagu da Sakaba sun nuna min goyon baya zahiri, tare da bukatar in fito domin in tsaya takara saboda in basu ingantaccen wakilci, kamar yadda suka jaddada mini cewa ni ke da muruba da ta dace da bukatarsu saboda suna da yakinin cewa zan iya basu jagorancin da suke bukata a Majalisar Wakilai.

Wannan jita-jita tunani ne kawai na wasu mutane kuma ba gaskiya bane"

Alh Kabir Tukura, Matshi ne da ya tsunduma cikin siyasar kasar Zuru a daidai lokaci da fagen siyasar Najeriya ke bin kidan kalangun bukatar Matasa, shi ma Tukura ya shigo filin domin ya taka rawarsa a fagen na siyasa a karkashin jam'iyar APC.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN