Yan takara a karkashin
jam’iyyar APC na ci gaba da nuna dari-dari da shuwagabannin jam’iyyar,
biyo bayan tsadar kudin tikitin tsayawa takara da jam’iyyar ta sanar.
Rahotannin da NAIJ.com ta tattara a Abuja, a ranar asabar, na nuni da
cewa yan takara a jam’iyyar, da suka nuna sha’awar tsayawa takara a
matakin gwamna, majalisun dokoki na kasa da ma shugaban kasa, na bayyana
damuwarsu bisa tsadar da tikitin yayi.
Rahotanni sun bayyana cewa yan takarar sun bukaci da a rage kudaden da
aka sanya.
A baya bayan nan ne dai kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta APC, ya fitar
da kudin tikitin tsayawa takarar shugaban kasa akan Naira Miliyan 55,
wanda ya haura Naira Miliyan 12 da jam’iyyar PDP ta sanyawa nata
Wadanda suka bayyana sha’awarsu ta tsayawa takarar majalisun dokoki na
jihohi a jam’iyyar, za su biya Naira miliyan daya dadubu dari, sabanin
na jam’iyyar PDP da zasu biya Naira 600,000. Ya yin da yan takarar
majalisun tarayya zasu sayi tikitin akan kudi N3.8m., sabanin na
jam’iyyar PDP da zasu biya N1.5m.
A bangaren masu sha’awar tsayawa takara a matakin majalisar dattijai,
jam’iyyar ta APC ta sa kudin tikitin akan N8.5m, sabanin N3.5m da
jam’iyyar PDP ta sanyawa yan takarar majalisar dattijai a jam’iyyar.
An bukaci masu sha’awar tsayawa takarar gwamna a jam’iyyar APC da su
biya kudin tikiti N22.5m sabanin N6m da PDP ta sanyawa tikitin tsayawa
takarar gwamnan a jam’iyyarta.
Wani mamba a kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC a matakin kasa, wanda
ya zanta da manema labarai dangane da rade-raden da ke yawo na wasu yan
takara a jam’iyyar na iya sulalewa saboda tsadar tikitin, ya ce
jam’iyyar na akan bakanta, ba zata rage farashin komai ba.
Wani tankarar majalisar tarayya a karkashin jam’iyyar ya ce tsadar
tikitin ba zata lalata shirye shiryen da aka rigaya akayi ba, sai dai
zasu yi zama na musamman, don tsara yadda lamarin zai kasance.
“Zamu bukaci jam’iyyar da ta sauko da wannan farashin nata, ko kuma ta
fuskanci janyewa daga mutane da dama, don kuwa tsadar tikitin ta yi
yawa,” a cewar sa. Read more: https://hausa.naija.ng/1189771-tsadar-tikiti-da-alama-apc-za-ta-rasa-yan-takara-a-zaben-fitar-da-gwani.html#1189771
Yan takara a karkashin jam’iyyar APC na ci gaba da nuna
dari-dari da shuwagabannin jam’iyyar, biyo bayan tsadar kudin tikitin tsayawa
takara da jam’iyyar ta sanar. Rahotannin da NAIJ.com ta tattara a Abuja, a
ranar asabar, na nuni da cewa yan takara a jam’iyyar, da suka nuna sha’awar
tsayawa takara a matakin gwamna, majalisun dokoki na kasa da ma shugaban kasa,
na bayyana damuwarsu bisa tsadar da tikitin yayi.
Rahotanni sun bayyana cewa yan takarar sun bukaci da a rage
kudaden da aka sanya. A baya bayan nan ne dai kwamitin gudanarwa na jam’iyyar
ta APC, ya fitar da kudin tikitin tsayawa takarar shugaban kasa akan Naira
Miliyan 55, wanda ya haura Naira Miliyan 12 da jam’iyyar PDP ta sanyawa nata
Wadanda suka bayyana sha’awarsu ta tsayawa takarar majalisun dokoki na jihohi a
jam’iyyar, za su biya Naira miliyan daya dadubu dari, sabanin na jam’iyyar PDP
da zasu biya Naira 600,000. Ya yin da yan takarar majalisun tarayya zasu sayi
tikitin akan kudi N3.8m., sabanin na jam’iyyar PDP da zasu biya N1.5m.
A bangaren masu
sha’awar tsayawa takara a matakin majalisar dattijai, jam’iyyar ta APC ta sa
kudin tikitin akan N8.5m, sabanin N3.5m da jam’iyyar PDP ta sanyawa yan takarar
majalisar dattijai a jam’iyyar. An bukaci masu sha’awar tsayawa takarar gwamna
a jam’iyyar APC da su biya kudin tikiti N22.5m sabanin N6m da PDP ta sanyawa
tikitin tsayawa takarar gwamnan a jam’iyyarta. Wani mamba a kwamitin gudanarwa
na jam’iyyar APC a matakin kasa, wanda ya zanta da manema labarai dangane da
rade-raden da ke yawo na wasu yan takara a jam’iyyar na iya sulalewa saboda
tsadar tikitin, ya ce jam’iyyar na akan bakanta, ba zata rage farashin komai
ba.
Wani tankarar majalisar tarayya a karkashin jam’iyyar ya ce
tsadar tikitin ba zata lalata shirye shiryen da aka rigaya akayi ba, sai dai zasu
yi zama na musamman, don tsara yadda lamarin zai kasance. “Zamu bukaci
jam’iyyar da ta sauko da wannan farashin nata, ko kuma ta fuskanci janyewa daga
mutane da dama, don kuwa tsadar tikitin ta yi yawa,” a cewar sa.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng