• Labaran yau

  An ba hammata iska wajen wani taron jam'iyar APC a jihar Adamawa, karanta dalili


  Mun samu labari yau dinnan cewa wani mummunan rikici ya barke tsakanin wasu manyan Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa a karshen makon nan.

  Ana tunani rigimar ba ta rasa nasaba da zaben fitar da gwani da za ayi. Wasu ‘Yan iskan gari ne da ake tunani su na tare da Mai Girma Gwamna Muhammadu Jibrilla Bindow su kayi kokarin jawo fitina domin nuna rashin amincewar su da tsarin da Uwar Jam’iyyar APC ta ke shirin kawowa. Jam’iyyar APC na kokarin yin amfani da zaben kato-bayan-kato wajen fitar da ‘Yan takarar ta a zaben 2019.

  Gwamnonin APC da dama dai ba su yi na’am da wannan tsari ba wanda hakan ya fara kawo tashin hankali a wasu wurare.

  Daily Trust ta rahoto cewa wasu ‘Yan daba da ke goyon bayan Gwamna Bindow sun rusa ofishin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir David Lawal. Hakan yayi sanadiyyar raunuka da kuma barnata motoci da dama. ‘Yan Tawaren Jam’iyyar APC a Adamawa karkashin Dimas Ezra sun zargi Gwamna da kitsa wannan aiki.

  Manyan APC a Jihar irin su Murtala Nyako, Babachir Lawal da Nuhu Ribadu su na tare da bangaren Taware na Ezra. Wadannan 'Yan daba sun fasa taron da aka shirya ne bayan sun ji ana kokarin amincewa da zaben kato-baya-kato wajen bada tutar Jam'iyya. Shi dai Gwamna Muhammadu Jibrilla yace ko kadan babu hannun sa.
   

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  Hausa.naij.ng
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An ba hammata iska wajen wani taron jam'iyar APC a jihar Adamawa, karanta dalili Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });