A yayin da jama'a ke cigaba da jiran hukumar zabe mai zaman
kanta (INEC) ta sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Osun da aka kammala
jiya, akwai yiwuwar sai an je zagaye na biyu domin tantance waye ya lashe zaben
gwamnan jihar.
Tuni dai masana doka suka kammala bayyana hujjojin a kan
cewar ba zai yiwu INEC ta bayyana dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe
zaben ba saboda adadin kuri'un da suka lalace a zaben sun fi adadin kuri'u 300
da suka bashi rinjaye a zaben.
Wani dalili da masanan suka kara bayarwa shine cewar sai dan
takara ya sami kashi 25% na biyu bisa ukun (2/3) kananan hukumomin jiharsa
kafin a bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara. A baya naij.com ta sanar da
ku cewar sakamakon Karamar Hukuma guda kadai ya rage a gane wanda zai lashe zaben
Jihar Osun.
Wannan Karamar Hukuma dai ita ce Osogbo inda nan ne babban
Birnin Jihar Osun kuma mafi yawan Jama’a a kaf Jihar. Jaridar Premium Times ta
rahoto cewa da zarar an samu cikakken sakamakon Garin Osogbo za a gane wanda
zai zama sabon Gwamnan Jihar Osun.
Yanzu dai an kawo sakamakon kananan Hukumomi 29 cikin 30 da
ake da su. Hukumar INEC ta tabbatar da cewa APC tana da kuri’u 224, 488 yayin
da Jam’iyyar adawa na PDP ke da kuri’a 236, 784. Hakan na nufin PDP ta sha
gaban APC da kuri’a 12, 000. Yanzu dai sakamakon Osogbo kurum ake sa rai ya
fito Jam’iyyar APC ta samu nasara a Kananan Hukumomi 15 yayin da PDP ta lashe
Kananan Hukumomi 11 kacal.
ADP kuma ta samu nasara a Karamar Hukumar Iwo yayin da SDP
ta kawo Kananun Hukumomin Ife ta tsakiya da Gabas. Yanzu haka dan takarar PDP,
Sanata Ademola Adeleke, keda mafi rinajen kuri'u a sakamakon da aka kamma
tattarawa duk da an hada da sakamakon zaben karamar hukumar Osogbo da ake ta
jira.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI