Gwamna Abdulazeez Yari ya bayyana cewa daga 2011 kawo yanzu
an kashe mutane sama da 2000 a cikin Jihar Zamfara. Gwamnan ya bada adadin
wadanda aka hallaka a Jihar ne a makon nan.
Abdulaziz Yari ya
tabbatar da cewa mutum sama da 2, 300 aka rasa cikin shekaru kusan 8 da yayi
yana mulki Jihar Zamfara. Gwamnan ya bayyana wannan ne wajen wani taro da
Gwamnati ta shirya da al’ummar Jihar a cikin Garin Gusau. Ministan yada labarai
Lai Mohammed da kuma Ministocin tsaro da na harkar ruwa watau Mansur Dan-Ali da
Suleiman Adamu sun halarci taron.
Yari yace rikicin ya jawo an samu ja-baya kwarai da gaske
wajen harkar noma a Jihar Zamfara. Gwamnan ya kuma sanar da cewa an rasa tumaki
fiye da 25, 000 daga lokacin da rikici ya barke a Zamfara kawo yanzu. Yari ya
nuna takaicin sa ganin cewa kusan kaf mutanen Zamfara Musulmai ne amma ake
samun irin wannan kashe-kashe.
Gwamna Yari yace a 2014, kaf Jihar Zamfara Sojoji ba su wuce
24 inda shi kuma Ministan labarai ya nuna cewa an fara samun saukin rikici a
Yankin. Ministan tsaro na kasar ya nemi jama’a su daina fadawa masu tada
rikicin asirin Jami’an tsaro.
Kwanaki kun ji cewa wani Tsohon ‘Dan Majalisar Wakilan
Tarayyar Najeriya yace akwai rikici shigen irin na ‘Yan ta’addan Boko Haram a
Zamfara wanda yayi kira da Gwamnati ta dauki mataki.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI