A lokacin da Sanatan yake magana da wakilin, ya kara jaddada
cewar ba zasu bari Saraki ya cigaba da mulkar su a matsayin shugaban majalisar
dattawa ba, tunda har ya canja sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party
PDP.
A cikin satin nan ne Sanatocin jam'iyyar APC suka gana da
shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, domin neman mafita akan Saraki.
Sanatan yace, "Muna da labarin cewa suna kokarin su hade majalisun biyu,
mu kuma baza mu taba yarda hakan ya faru ba.
Saboda yanzu haka Saraki ya san
cewa mun cika adadin da zamu iya cire shi daga kujerar shi. Saboda haka da mun
samu wata dama zamu yi amfani da ita domin tsige shi daga kujerar ta shi."
A martanin da Saraki
ya mayar ta bakin mai bashi shawara a fannin yada labarai, Yusuph Olaniyonu, ya
yi Allah wadai da zargin da Sanatan yake yi, inda ya bayyana cewa wadanda suke
so su tsige shi din sune babbar matsalar kasar nan ba shi ba.
Ya ce, "Muna
kokari muga mun rike mukaman mu, saboda da yawa a cikin masu son tsige ni
maciya amana ne, don haka baza mu bari hakan ya faru ba. Da akwai da yawa a
cikin su wanda ya kamata ace yanzu haka suna gidan kurkuku, saboda irin
abubuwan da suka aikata. Amma saboda kariya da suke samu daga wurin gwamnati
shine yasa har suke da bakin magana."
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Haausa.naij.ng