Fitacciyar 'yar wasan Hausan nan Hauwa S. Garba wacce aka fi
sani da 'Mama' tana daya daga cikin wanda tauraruwar su ke haskawa a 'yan wasan
Hausa a yanzu Fitacciyar 'yar wasan Hausan nan Hauwa S. Garba wacce aka fi sani
da 'Mama' tana daya daga cikin wanda tauraruwar su ke haskawa a 'yan wasan
Hausa a yanzu.
A zantawar da manema labarai suka yi da ita, yarinyar 'yar
shekara 19, kuma haifaffiyar jihar Legas, ta bayyana irin abubuwan da suka ja
ra'ayinta ta shiga harkar fim din Hausa. 'Yar wasan ta bayyana yanda ta tsinci
rayuwar ta cikin shirin fim din Hausa.
Tace ta tsinci kanta a cikin shirin fim din Hausa ne a
lokacin da ta hadu da shahararren mawakin nan na siyasa, Dauda Kahutu Rarara.
Ta ce kafin ta hadu da Rarara, tana zaune da Aunty ta a jihar Kano. Mu ma'abota
kalon shirin fim din Hausa ne, ta dalilin haka naji wasan ya fara kwanta mini a
rai, kuma naji ina sha'awar shiga harkar. Bazan manta ranar da muke hirar 'yan
fim din Hausa da wata 'yar uwata, na fada mata cewar ina sha'awar shiga harkar
fim. Sai take ce mini ai ta san Rarara, daga nan tayi minijagora zuwa wurin
shi.
Da muka hadu dashi sai yake fada mini cewar shi baya shirin
fim, amma zai hada ni da wani wanda ya sani. Ba a dade ba ya hadani da
shahararren mai shirya fina-finan Hausan nan Usman Mu'azu. TO tun daga nan na
fara fitowa a shirin fim din Hausa.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa..naij.ng