Mun samu labarin cewa wasu manyan mata da ma kanana sun fita
a saman manyan titunan jihar Imo dakea a kudu maso gabashin Najeriya a tsirara
domin yin zanga-zangar kin jinin gwamnati bisa cigaba da tsare Nnamdi Kanu da
ake cigaba da yi.
Su dai matan da suka fito da yawa sun yi ta rera wakokin kin
jinin gwamnati tare kuma da bayyana bukatar su ta a sako jagoran kungiyar nan
dake fafutukar ganin an raba kasar nan ta Indigenous People of Biafra (IPOB).
NAIJ.com ta samu cewa sai dai tuni jami'an 'yan sandan jihar
suka cafke matan kafin daga bisani da yawan su su tsere.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng