Mun samo daga Daily Trust cewa hukumar 'yan sanda reshen
jihar Katsina ta damke wata budurwa, Zinatu Abubakar mai shakaru 19 da tayi
yunkurin sace babur din wani matashi bayan ta dirka masa kwayoyi. Sanarwar da
jami'in hulda da jama'a na rundunar, Gambo Isa ya bawa manema labarai a ranar
Alhamis na Katsina na cewa. budurwar tana aiki ne tare da wasu gungun barayi da
suka dade suna adabar mutanen Katsina.
'Yan sanda sun damke wata budurwa mai yiwa 'yan acaba fashi
'Yan sanda sun damke wata budurwa mai yiwa 'yan acaba fashi Source: Facebook
Isa ya ce wanda ake zargin ta bawa mai babur din, Gide Wada kwayar ne a lokacin
da ya dauko ta daga Kofar-Kaura zuwa Sokoto Rima Quaters duk a garin Katsina.
Kakakin 'yan sandan ya ce mai babur din ya tsaya a lokacin
da ya fara ganin jiri bayan Zinatu ta bashi Chocolate a hanyarsu ta tafiya inda
zai kaita. Kamar yadda ya ce, bayan mai babur din ya tsaya sai wadanda ke aiki
tare da Zinatu, Abubakar da Chairman suka garzayo inda ya ke su kayi kokarin
kwace babur din. Ya yi bayannin cewa barayin zun ruga cikin daji yayin da suka
lura hayaniyar da su keyi yana janyo hankalin mutane.
Mutanen daga baya sun cafke Zinatu kuma suka mika ta ga
jami'an yan sanda. Isa ya yi ikirarin cewa wanda ake zargi da laifin ta amsa
laifinta kuma ta kara da cewa ta dade tana aikata irin wannan laifin a Kaduna
da Kano. Daga karshe ya shawarci masu achaba su guji karban abinci ko abin sha
daga mutanen da basu sani ba don gudun fadawa cikin irin wannan tarkon da zai
janyo ayi musu fashi.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa,naij,ng