An zargi wani jami’in dan sanda da harbe wani direban motar
bus, Mohammed Dajji, har lahira saboda yaki ba da cin hancin N50. Jaridar
Premium Times ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a jihar Taraba a ranar Juma’a,
31 ga watan Agusta.
Wani idon shaida da yayi magana kan sharadin boye sunasa
yace jami’in dan sandan ya harbi direban a tashar bincike dake kauyen Maisamari
a Nguroe saboda yaki bashi cin hanci N50. Fusatattun mazauna yankin da abun ya
faru a idanunsu sun far ma jami’in dan sandan.
A baya NAIJ.com ta ruwaito cewa yan sanda sun kama wani
jami’in kwastam kan laifin harbin wani mai mota a tashar Iya-Afin Badagry a
ranar Laraba, 29 ga watan Agusta. Majiyoyin yan sanda sun bayyanawa kamfanin
dillancin labaran Najeriya (NAN) a Badagry cewa jami’in kwastam din wanda aka
boye sunansa ya harbi wani mutum a kafadarsa na dama saboda yaki tsayawa a
bincike shi.
A cewar majiya, mai motan wanda ke fitowa daga Seme Border,
yaki tsayawa a inda ake duba motoci don haka sai jami’in ya bude masa wuta inda
abun ya same shi a kafadarsa na dama.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng