Yan acaba a Akure na jihar Ondo, sun gudanar da wata kasaitacciyar zanga-zanga bayan motar jami'an NSCDC ta kade wani dan acaba dauke da fasinja 2, lamari da ya yi sanadin mutuwar dan acaba, yayin da aka kwantar da fasinjan su 2 a mawuyacin hali a Asibitin gwamnati da ke Akure ranar Laraba.
Sakamakon haka ne yan acaba a birnin Akure suka fara zanga-zangar nuna rashin amincewa da yadda direban motar NSCDC ya banke dan acaba da mota lamari da ya sa dan acaba ya mutu.
Yan acaban dai sun dauki gawar dan uwansu wanda aka kashe suka kai shi ofishin NSCDC wanda ke kallon Gidan Gwamnatin jihar Ondo.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira