Jami’an yan sandan dake yaki da fashi da makami a jihar Imo
sun kama wani gawurtaccen dan kungiyar asiri kuma makashi, Chijioke Ogbonna
wadda aka fi sani da Ogotiti. Yayinda yan sanda suka gurfanar da shi a ranar
Asabar da ya gaata, Ogotiti ya fadama manema labarai cewa ya kashe mutane uku
tunda ya shiga kungiyar asiri a shekarar 2014. Matashin mai shekaru 23 wanda ya
kasance dan makarantar Federal Polytechnic, Nekede, yace kudirin da ya dauka na
daukar fansa ne ya kai shi ga kashe mutane uku, daya daga cikinsu ya kasance
dan kungiyar adawarsu.
Ogbotiti wadda ya kasance dan asalin garin Umuejije, karamar
hukumar Isialangwa ta kudu dake jihar Abia yayi bayanin cewa babban makami da
yake amfani da shi ya kasance bindigar gargajiya.
Jami’in hulda da jama’a na rundunaar yan sandan jihar Imo,
Andrew Enwerem ya bayyana mai laifin a matsayin gawurtaccen dan kungiyar asiri
da fashi da makami, ya kara da cewa jami’an SARS ne suka kama shi a ranar 19 ga
watan Agusta a Ama-Hausa dake yankin Owerri, babban birnin jihar. Enwerem yace
yan sanda na neman mai laifin tun a 2014 kan zargin rawar ganin da yake takawa
wajen aikata ayyukan laifi.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng