Dalili da ya sa nike son yin takarar dan Majalisar B-kebbi,Kalgo da Bunza - Abu Najakku


Dan takaran kujerar dan Majalisa mai wakiltar Birnin kebbi, Kalgo da Bunza a Zauren Majalisar tarayya Alh. Abu Najakku, ya ce a shirye ya ke ya bayar da ingantacce tare da nagartaccen wakilci ga jama'ar Mazabarsa matukar aka zabe shi. Ya kuma ce matukar dai za'a zabeshi kuma ya ki dawowa gida domin ya yi cudani da jama'arsa, to kada Allah ya bashi kujerar.

Abu Najakku ya ce " Na shiga wannan Siyasa ne domin in yi ma shugaba Buhari hidima, domin mutumin kirki ne wanda ke kokarin ciyar da Najeriya gaba, amma akwai wadanda suka sha alwashin ganin sun kawar da manufofinsa na alhairi ga talaka.

Sakamakon haka nike bukatar in yi masa hidima domin ganinin ya ci nassarar manufofinsa. Kowa ya san Buhari ba barawo bane kuma baya bari a yi satar dukiyar tallakan Najeriya. Ya yi ayyuka da yawa da suka hada da hanyar  Jirgin kasa daga Lagos zuwa Abuja, hakazalika layin Dogo watau hanyar jirgin kasan za ta bi har ta jhar Kano da jihohin Zamfara, daga bisani hanyar Jirgin zai iso har Sokoto da Kebbi".

Dan takaran ya ziyarci wasu garuruwa domin sada zumunta da gaisuwar Sallah. Daga cikin wurare da ya ziyarta har da garin Makera, Maurida, Gawassu, sai a cikin garin Birnin kebbi, dan takaran ya ziyarci Nassarawa 2 da Nassarawa 1 daga bisani ya zarce zuwa Marafa ward inda ya gabatar da kansa tare da bayyana aniyarsa ta yin takaran kujerar dan Majalisa mai wakiltar Birnin kebbi, Kalgo da Bunza a karkashin jam'iyar APC ga shugabanni da Ex-co na jam'iyar APC na wadannan Mazabu da yaziyarta..

Ku kasance tare da sashen mu na Siyasa, domin samun labari da suka shafi Siyasar jihar Kebbi da Najeriya. 

Daga Isyaku Garba


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN