Tikari sun damfari mahajjatan jihar Kebbi 8 kudin guzurinsu a kasar Saudiyya

Rahotanni daga kasar Saudiya sun ce Mahajjata takwas ne daga jihar Kebbi suka fada hannun Tikari yan damfara a kasar Saudiya wadanda suka cuce su ta hanyar damfararsu kudaden su na guzuri BTA .

Kampanin dillancin labarai na Najeriya NAN ta ambato cewa shugaban Mahajjatan jihar Kebbi a birnin Madina Alh. Abubakar Argungu ,ya shaida wa manema labarai haka ranar Alhamis.

Abubakar ya bukaci jami'an aikin Hajji na jihar Kebbi su dukufa wajen ayyukansu tare da bukatar a bullo da Banki daya da zai dinga karbar kudin Hadaya, haka zalika ya bukaci a kara yawan mata da ke cikin aikin taimaka wa Mahajjata a kasar Saudiya.

Bayanai sun nuna cewa wadanda aka fi cuta sune tsofaffi, ta hanyar harkar canjin kudi. Hakazalika bayanan su nuna cewa Tikarin sukan yaudari Mahajjatan ne bayan sun fito daga dakunan Hotel da suka sauka, daga bisani sai su yaudaresu, kuma a neme su kasa ko sama sun arce.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN