'Yan sanda a jihar Imo
sun cafke wasu mata da miji Ugochukwu Nwachukwu da Glory Nwachukwu bisa
alifin sayar da jaririnsu dan watanni hudu da haihuwa kan kudi Naira
dubu dari hudu (400,000).Da yake holar iyayen jaririn a shelkwatar ‘yan
sanda ta kasa reshen jihar ta Imo dake Owerri a jiya Laraba, kwamishinan
‘yan sanda na jihar Dasuki Galadanchi, ya ce iyalan 'yan yankin Umueme
Obike dake a karamar hukumar Ngor Okpala.
Kuma bayan aika-aikar sayar da dan nasu da suka yi, sun sake hada baki
suka yaudari wata mata suka sace yara mata 'ya'ya biyu suka sayar da su.
Kwamishinan ya kara da cewa, “Jami’an rundunar masu yaki da ‘yan garkuwa
da mutane ne suka damko su a ranar 20 ga watan Yuli a yankin Owerre-Nta
dake karamar Isiala Ngwa cikin jihar Abia. Tuni suka amince da aikata
laifin yin safarar mutane da sauran laifuka a fadin jihar ta Imo.”
Galadanchi ya kuma shaida cewa yanzu haka rundunar ‘yan sandan na cigaba
da farautar ragowar abokan aikata laifukan na kungiyar da suka tsere.
Sai dai Ugochukwu ya shaidawa manema labarai cewa ya sayar dan nasa kan
kudi Naira N400,000 ne saboda tsananin matsin rayuwa da suke fama da shi
don ta siyi babur. Read more: https://hausa.naija.ng/1185350-kaico-iyaye-sun-hada-baki-sun-sayar-da-jaririnsu-n400000.html#1185350
'Yan sanda a jihar Imo sun cafke wasu mata da miji Ugochukwu
Nwachukwu da Glory Nwachukwu bisa alifin sayar da jaririnsu dan watanni hudu da
haihuwa kan kudi Naira dubu dari hudu (400,000).Da yake holar iyayen jaririn a
shelkwatar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar ta Imo dake Owerri a jiya Laraba,
kwamishinan ‘yan sanda na jihar Dasuki Galadanchi, ya ce iyalan 'yan yankin
Umueme Obike dake a karamar hukumar Ngor Okpala.
Kuma bayan aika-aikar sayar da dan nasu da suka yi, sun sake
hada baki suka yaudari wata mata suka sace yara mata 'ya'ya biyu suka sayar da
su. Kwamishinan ya kara da cewa, “Jami’an rundunar masu yaki da ‘yan garkuwa da
mutane ne suka damko su a ranar 20 ga watan Yuli a yankin Owerre-Nta dake
karamar Isiala Ngwa cikin jihar Abia.
Tuni suka amince da aikata laifin yin safarar mutane da
sauran laifuka a fadin jihar ta Imo.” Galadanchi ya kuma shaida cewa yanzu haka
rundunar ‘yan sandan na cigaba da farautar ragowar abokan aikata laifukan na
kungiyar da suka tsere. Sai dai Ugochukwu ya shaidawa manema labarai cewa ya
sayar dan nasa kan kudi Naira N400,000 ne saboda tsananin matsin rayuwa da suke
fama da shi don ta siyi babur.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng
Tags:
LABARI