A yayin da zaben 2019 ke karatawo, gwamnatin shugaba
Muhammadu Buhari ta fitar da wasu muhimman aiyuka shida da tayi a kowanne
yankunan Najeriya da zasu kawo cigaba ga rayuwan al'ummar yankunan.
1. Lagos Ibadan express road (Kudu maso Yamma) Babban titin
Legas zuwa Ibadan yana daya daga cikin aiyukan da gwamnatocin baya suka dade
suna ikirarin zasu yiwa gyara tare da fadadawa sai dai a yanzu gwamnatin
shugaba Buhari ta tasar wa aikin gadan-gandan. A wata rahota da Daily Trust ta
wallafa, gwamnatin tarayya ta ware N64 biliyan don karasa wata bangare na
aikin. Ministan makamashi, aiyuka da gidaje, Babatunda Fashola yace gwamnati ta
amince da ware kudin ne saboda muhimmancin da hanyar keda shi ga matafiya.
2. Babban titin Kano zuwa Maiduguri (Arewa maso Gabas/Arewa
maso Yamma) Babban titin Kano zuwa Maiduguri tana daya daga cikin manyan
aiyukan titi da gwamnatin shugaba Buhari ta fara gudarwa da kudin Sukuk.
Ministan Makamashi, ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola yace gwamnati ta mayar
da hankali kan ayyukan ne saboda cika wa al'umma akawuran da aka dauka yayin
yakin neman zabe.
3. East-West Road (Kudu maso Kudu/Kudu maso Gabas) Ministan
Sufuri, Rotimi Amaechi yace 'yan kwangilar dake aikin titin na bukatar N100
biliyan domin kammala gyra da fadada titin. Mr Ameachi tare da Ministan
Neja-Delta, Uguru Usani sun fadi hakan ne yayin da suka kai ziyarar duba aikin
da aka fara da Warri zuwa Eleme Junction kamar yadda Premium Times ta wallafa.
4. Jami'ar Maritime ta Jihar Delta (Kudu maso Kudu) An kafa
wannan jami'ar ne ta musamman saboda koyar da darussa masu alaka albarkatun
ruwa. Tuni jami'ar ta fara daukan dalibai masu karatun digiri a sassa daban da
suka hada da karatun Injiniya da sauransu.
5. Jiragen Kasa na zamani (Babban birnin tarayya Abuja) An
bayar da kwangilar gina tasha da saya jiragen kasar ne tun watan Mayu na 2007 a
zamanin mulkin shugaba Olusegun Obasanjo sai an dakatar da aikin saboda rashin
kudi. Gwamnatin shugaba Buhari ta farfado da aikin inda ta bayyana cewa an
kammala shimfida titin jirgin da kuma tashoshi 12 a yayinda ake cigaba da
karasa sauran ayyukan.
6. Kamfanin Karafa ta Ajaokuta (Arewa ta tsakiya) A
yunkurinta na farfado da masana'antu da kamfanoni da suka dade basu tabbuka
wani abin azo a gani, gwamnatin shugaba Buhari ta ware mukuden kudade don
gyaran kamfanin karafar dake jihar Kogi.
7. N Power N power shiri ne wadda gwamnatin shugaba Buhari
ta bullo dashi saboda bawa matasa horo kan sana'o'i daban-daban ta yadda zasu
kasance masu dogaro da kansu kana a rage matsalar rashin aiyukan yi da ake fama
dashi a kasar. A karkashin shirin ana koyar da matasa sana'o'i kamar aikin noma
da kiwo, aikin malanta, kiwon lafiya da sauransu na tsawon shekaru biyu kafin a
yaye su domin su cigaba da sana'oin da suka koya.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng