Hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewar ta kama, Maje Lawan,
kwamandan kungiyar Boko Haramda ta dade tana nema ruwa a jallo.
A cewar darektan yada labarai na hukumar sojin Najeriya,
Birgediya janar Texas Chukwu, Maje ne na 96 a jerin sunayen 'ya'yan kungiyar
Boko Haram da hukumar ke nema ruwa a jallo.
An kama shi ne a Banki dake jihar Borno. Chukwu ya bayyana
cewar an kama Maje ne bayan ya yi basaja ya sumama cikin sansanin 'yan gudun
hijira.
Yanzu haka yana hannun hukumar ta soji domin amsa tambayoyi
kafin mika shi ga hukumar da tafi cancanta. Kazalika Chukwu ya bayyana yadda
rundunar soji tayi nasarar kashe wasu mayakan kungiyar Boko Haram biyu a kauyen
Malari bayan kaddamar da wani harin kwanaton bauna a kan 'yan ta'addar. An samu
wasu kekeunan hawa 10 tare da 'yan ta'addar.
A wani labarin mai nasaba da wannan, Chukwu ya bayyana cewar
dakarun soji sun fatattaki wasu 'yan ta'adda daga maboyar su dake
Gbamjimba-Akor dake karamar hukumar Guma ta jihar Benuwe.
Ya kara da cewar wasu daga cikin 'yan ta'addar su mutu, sai
dai bai ambaci adadinsu ba.
An samu babbar bindiga samfurin AK-47 guda daya da
alburusai da kuma Baburan hawa 5.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng