• Labaran yau

  Wani matashi ya fallasa yadda suke kashe Hausawa da Fulani a Taraba


  A wani irin salo dake zaman tamkar dabawa kai wuka a ciki, wani matashi mai suna Panshak Isaiah ya je a kan shafin sa na dandalin sadarwar zamani na Fezbuk inda ya labarta yadda yace suna kashe Hausawa da Fulani tamkar awaki a jihar Taraba.

  Matashin dai ya rubuta cewa "Karshen su yazo yau (watau Hausawa da Fulani), gamu nan muna ta kashe Hausawa da Fulani a garin Kunini kamar awaki".

  NAIJ.com ta samu cewa irin wadannan kalaman na nuna kiyayya na zaman tamkar wasu guma-guman dake rura wutar rikicin kabilanci a yankunan jahohin Arewa ta tsakiya irin su Taraba din. 

  Tuni dai jama'a da dama da suka ga rubutun na matashin suka yi Allah-wadai da shi tare da jan hankali da kira ga jami'an tsaro da su tabbatar da doka ta hau kan matashin domin hakan ya zama izina ga 'yan baya. Abun zura ido agani yanzu dai shine ko jami'an tsaro za su farka daga baccin da suke yi domin ganin doka tayi aiki akan matashin da ma sauran masu irin tunani da halayyar sa a ko'ina suke a fadin kasar.
   

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu 
  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
  Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  Hausa.naij.ng
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wani matashi ya fallasa yadda suke kashe Hausawa da Fulani a Taraba Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama