• Labaran yau


  Wani Gandiroba zai yi kwanan gidan yari


  Wani jami'in aikin gidan yari (Gandiroba) ya gurfana gaban kotu bisa laifin damfara. Adamu Usman shi ne wanda yayi karar Abubakar Jidda Usman a gaban wata kotu dake zamanta a yankin Doma dake jihar Gombe.

  Lauyar mai karar Rahina Ibrahim Talle ta gabatar da karar gaban kotu tare da cewa Abubakar ya yaudari wanda take karewa kudi har Naira dubu 250,000 da sunan zai sama masa aiki a hukumar tsaro ta civil defense.

  Ta kara da cewa takardun yarjejeniyar daukan aiki da Abubakar ya kawowa Adamu an gano na jabu ne bayan da yaje tantancewa domin daukarsa aikin na civil defense Bayan rashin nasara da yayi a wajen tantancewa ne daga bisani Adamu ya bukaci da a ba shi kudinsa tunda dai in ba kira ba abinda zai ci gawayi, nan ne tirka-tirka ta soma.

  Abubakar ya amsa cewa tabbas Adamu ya ba shi kudi har Naira dubu 250,000 amma ya musanta zargin da ake cewa ya ba shi takardun bogi. Alkalin kotun mai shari'a Aminu Haruna ya tambayi Abubakar da yayi wa kotu cikakken bayani akan nawa ake kashewa kafin a samu aiki a hukumar ta Civil defense, sai dai wanda ake karar ya bayyana cewa shi ma bai sani ba.

  Daga nan ne mai shari'ar ya umarci da a tisa keyarsa zuwa gidan kaso har sai 9 ga watan Agustan nan domin sake cigaba da sauraren shari'ar.
   

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu 
  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
  Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  Hausa.nai.ng
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wani Gandiroba zai yi kwanan gidan yari Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama